✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka miyar agushi irin na Ibo

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar agushi kamar yadda Ibo ke girka…

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar agushi kamar yadda Ibo ke girka nasu. Mata da dama na girka miyar agushi ta hanyoyi daban-daban. Wadansu ma zubawa kawai suke yi da sunan an yi miyar. Yana da kyau mace ta koyi yadda za ta rika canja salon girke-girke a koyaushe.

Abubuwan da za a bukata

  • Agushi
  • Manja /man gyada
  • Ganyen Uziza (za a iya samunsa a inda Ibo suke a kasuwa)
  • Tattasai
  • Albasa
  • Garin kifin ‘cry fish’
  • Daddawa
  • Kifi
  • Nama
  • Kayan dandano
  • Kayan kamshi

 

Hadi

A kwaba agushi da ruwa yadda zai dan yi kauri sannan a dora tukunya a wuta a zuba man gyada kadan da manja kadan. Bayan haka, sai a mulmula kwabin agushi zuwa kananan mulmule sannan a zuba albasa  a rika jefawa a cikin man. Haka za a rika jefawa sannan a juya da cokali na tsawon mintuna uku sai a zuba ruwa a cikin tukunyar da ake soya agushin. Sai a rufe da marufin tukunyan har sai ya tafasa sannan sai a dan farfasa agushin da cokali a zuba dafaffen busasshen kifi da dafaffan nama da  yankakken ganyen Uziza da kayan dandano da na kamshi sannan a rufe. Bayan mintuna goma zuwa sha biyu sai a sauke.