✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka Alalen Doya

Assalamu Alaikum Uwargida, barka da wannan lokacin. Yaya azumi? Yau a filin namu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake girka Alalen Doya

Assalamu Alaikum Uwargida, barka da wannan lokacin. Yaya azumi?

Yau a filin namu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake girka Alalen Doya.

Da farko dai ga kayayyakin da uwargida ke bukata don yin alalen:

Doya

Manja

Man gyada

Attarugu

Albasa

Kifin karafish

Kayan kamshi

Kwai

Gishiri

Sinadarin dandano

Leda/gwangwani

 

Yadda ake yi:

Uwargida za ki fara gurza doya sai ki zuba albasa da atturugu a ciki ki  markada.

Sai ki dafa kwai ki yayyanka shi ki ajiye a gefe.

Sannan ki sake yanka wata albasar ki zuba a kan markaden nan.

Sai ki dauko sinadarin dandano da gishiri da kayan kanshi da nikakken kifin karafish ki zuba a kai.

Daga nan sai ki zuba manja da man gyada a kai ki juya sosai.

Sannan sai ki dauko gwangwani ko leda ki rika zuba hadin alalen nan a ciki sannan ki dauko yankakken dafaffen kwai ki zuba a ciki.

Sai ki ajiye har sai kin gama sai ki zuba a tukunya yadda zai turara. Idan ya dahu sai ki sauke.

Shi ke nan alalen doya ya kammala.

A ci dadi lafiya.