✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake faten doya mai alayyahu

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake faten doya. Faten doya dai girki ne da…

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake faten doya. Faten doya dai girki ne da kowa ya san shi. Wani hanzari ba gudu ba, yadda wata za ta girka nata daban yake da yadda wata  za ta girka nata faten doyar. Wata idan ta yi wannan girkin sai a ga doyar daban da ruwa da manja ko kauri faten ba ya yi. Sai a ga manyan gobe ba su sha’awar cin abincin. Dole ne mata su dage su koyi nau’o’in girke-girke yadda manyan gobe za su rage yin kwadayi idan an je unguwa.

 

Abubuwan da ake bukata

•        Doya

•        Manja

•        Alayyahu

•        Nikakken ‘cray fish’

•        Albasa

•        Attarugu

•        Tumatir

•        Bandar kifi

•        Nama

•        Tafarnuwa

•        Citta

•    Magi

•    Kori

 

Hadi

A sami danyar doya a fere ta a yayyanka ta kanana sannan a wanke a ajiye a gefe. Bayan haka sai a samu ganyen alayyahu shi ma a yayyanka amma manya-manya a wanke da ruwan gishiri sannan a ajiye a gefe. A silala nama da albasa da gishiri kadan sosai sannan a sauke.

A dora tukunya a wuta sai a zuba manja sannan a zuba yankakkiyar albasa da tafarnuwa da garin citta da yankakken attarugu da tumatir. A yi ta gaurayawa har sai sun soyu. Sannan a zuba ruwan nama da naman da magi da kori a wanke bandar kifi a zuba da ‘cray fish.’ Idan ya dan tafaso sai a dauko wannan yankakkiyar doyar a zuba a ciki. Idan ta dahu ta yi laushi sai a samu muciyar tuwo a dan farfasa doyar sama-sama yadda ruwan zai yi kauri sannan a dauko yankakken alayyahu a zuba na tsawon minti biyu zuwa uku. Idan ya nuna sai a gauraya a sauke. A ci dadi lafiya.