✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake farfesun kan rago

Farfesun kan rago dadadden abincin marmari ne da ya zaga wurare daban-daban a fadin duniya kuma ake sha’awar shi. Bayan dadi a baki, farfesun naman…

Farfesun kan rago dadadden abincin marmari ne da ya zaga wurare daban-daban a fadin duniya kuma ake sha’awar shi.

Bayan dadi a baki, farfesun naman kan rago ya kunshi sinadarai da ke tsaftace jini da kitse mai wuyar narkewa a jikin dan Adam.

Shi ya sa yau muka yi muku tsarabar yadda ake yin farfesun kan rago:

Kayan hadi

 • Gyararre kuma wankakken kan rago
 • Kayan kamshi
 • Sinadarin dandano
 • Markadaddiyar albasa
 • Attaruhu (daidai da yadda ake so)
 • Garin girfa kadan (cinnamon)
 • Dakakkiyar daddawa kadan

Yadda ake yi

 1. A wanke naman kan ragon a zuba a tukunya
 2. A zuba ruwa da duk kayan hadi sai a rufe tukunyar ruf
 3. A dafa tsawon mintina 40
 4. Idan aka taba aka ji ya yi laushi sai a sauke.

Ana ci da burodo, gurasa, ko shinkafa.

A ci dadi lafiya.