Farfesun kan rago dadadden abincin marmari ne da ya zaga wurare daban-daban a fadin duniya kuma ake sha’awar shi.
Bayan dadi a baki, farfesun naman kan rago ya kunshi sinadarai da ke tsaftace jini da kitse mai wuyar narkewa a jikin dan Adam.
Shi ya sa yau muka yi muku tsarabar yadda ake yin farfesun kan rago:
Kayan hadi
- Gyararre kuma wankakken kan rago
- Kayan kamshi
- Sinadarin dandano
- Markadaddiyar albasa
- Attaruhu (daidai da yadda ake so)
- Garin girfa kadan (cinnamon)
- Dakakkiyar daddawa kadan
Yadda ake yi
- A wanke naman kan ragon a zuba a tukunya
- A zuba ruwa da duk kayan hadi sai a rufe tukunyar ruf
- A dafa tsawon mintina 40
- Idan aka taba aka ji ya yi laushi sai a sauke.
Ana ci da burodo, gurasa, ko shinkafa.
A ci dadi lafiya.