✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake fanken doya

Yadda ake fanken doya

Jama’a barkan mu da wannan lokaci. Yau a shafinmu na Girke-girken azumi za mu kawo muku yadda ake fanken doya.

Ga abubuwan da ake bukata domin hada shi:

– Doya

– Madara

– Fulawa

– Hodar ‘baking powder’

– Gishiri

– Kwai guda uku

– Bota

– Nikakken naman kaza

– Man gyada

– Tafarnuwa

– Albasa

– Attarugu

– Kayan dandano

Yadda ake hadin

  • A dora man gyada a tukunya a wuta ba mai yawa ba, idan ya yi zafi sai a zuba yankakkiyar albasa, tafarnuwa da attarugu a ciki a soya na minti daya.
  • A zuba nikakken naman kaza, a sa gishiri da kayan dandano, a motsa na tsawon minti 4 ko 5 sai a kashe wuta, a ajiye a gefe.
  • A fere doya, a yayyanka ta, a wanke a dafa, idan ta nuna sai a daddaka a zuba a kwano mai zurfi.
  • A zuba gishiri kaddan, da ‘baking powder’sai a juya sosai.
  • A zuba fulawa da kwai sai a juya sosai, sannan a zuba hadin nikakken naman kazan a ciki.
  • A zuba ruwan madara kadan-kadan har sai ya yi kauri daidai irin na fanke.
  • Sai a dora tukunya mara kama girki a wuta, idan ta yi zafi a zuba bota kaddan, sai a rika debo kullun doya ana zuba shi ta irin yanayin da ake so.
  • A bari ya nuna, sai a juya daya gefen shi ma ya nuna, sannan a kwashe.
    Za a dinga haka daya bayan daya, har sai kullun ya kare.
  • Shi ke nan an hattama fanken doya, sai ci lafiya.