Kayayyakin da ake bukata
Shinkafa
Karas
Koren wake da tattasai
Tattasai
Attarugu
Albasa
Nikakken nama
Sinadarin dandano
Kori
Tafarnuwa
Citta
Kifi
Yadda za a girka shinkafar
- A dora tukunya da ruwa a cikinta har sai ya tafasa.
- A dauko shinkafa a wanke a zuba a ciki.
- Idan ta dan tafasa kamar na minti 10 zuwa 15, sai a sauke a wanke da ruwa, a tsame ta a matsami ruwan ya tsane.
- Daga nan sai a samu danyen nama a nika shi.
- A sake dora wata tukunyar a wuta sannan a zuba man gyada a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai.
- Sannan sai a zuba nikakken naman a ciki a ci gaba da soya shi.
- Daga nan kuma sai a dauko citta da tafarnuwa da sinadarin dandano da kori sai a ci gaba da juya su, sannan a zuba su karas da koren waken da tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da murfi na tsawon minti 20, sannan a sauke shi.
- Sai a wanke kifi a ajiye shi.
- A zuba man gyada a tukunyar ya yi zafi, sai a soya kifi a ciki har sai kifin ya fara canja kala zuwa ruwan kasa kafin a cire ci daga wuta.