Barkanmu da warhaka uwargida da fatan ana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza. Wannan irin dahuwar ana yi wa maigida ne a lokacin da zai dawo daga tafiya. Bugu da kari, domin burge maigida yin irin wannan girkin shi ya fi cancanta. Da zarar mace ta iya girki, zai yi wuya a ga maigida yana cin abinci a waje koda a gidan biki ne zai gwammace ya dawo gida yaci na uwargidansa. Don haka sai a dage mata!
Kayan hadi
• Nikakkiyar kaza
• Garin burodi
• kwai
• Fulawa
• Attarugu
• Garin tafarnuwa
• Magi
• Kori
• Garin citta
• Masoro
Yadda ake hadin
Uwargida ta samu kaza ta cire kashin jikin kazar sannan ta nika ta. Bayan ta nika, sai ta zuba a kwano. Sannan ta zuba dakakken masoro da kori da garin citta da magi da garin tafarnuwa da dakakken attarugu sannan ta cakuda su sosai.
Bayan an yi haka, sai a mulmula hadin sannan a sa a cikin fulawa sannan a sake shafa mata garin burodi sannan sai a zuba ruwan kwai sannan a jefa a man gyada mai zafi a tukunyar tuya. Bayan ta soyu sai a tsame.
A ci dadi lafiya.