✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake burabuskon zamani

Yadda ake burabuskon zamani

Barkanmu da wannan lokacin, yau kuma a filin namu mun kawo muku yadda ake girka Burabusko irin dahuwar zamani.

Kayan hadi

– Garin kwaki

– Naman kaza

– Tumatir

– Albasa

– Tattasai

– Attarugu

– Koren tattasai

– Tafarnuwa

– Garin citta

– Bota

– Magi

– Man gyada

– Ruwa

Yadda ake hadawa

– A wanke naman kaza a yayyanka shi kanana.

– A markada tafarnuwa da attarugu, a zuba a cikin sai a kwaba sosai.

– A dora tukunya a wuta sai a zuba bota da man gyada kadan.

– Idan ta yi zafi sai a zuba markaden attarugu da tafarnuwa a soya sai a zuba naman kazan ana juyawa har sai ya soyu sosai.

– A zuba yankkaken koren tattasai da albasa da tumatir da ganyen albasa sai a juya sosai.

– A saukar daga wuta a ajiye a jefe.

– Sai a zuba garin kwaki a roba daban, sai a zuba ruwa kadan a jujjuya shi sosai kar ya hadu.

– A zuba hadin kazan a ciki sai a juya sosai.

– A barbada garin citta a juye sosai.

Shi ke nan sai ci!