Barkanmu da wannan lokacin, yau kuma a filin namu mun kawo muku yadda ake girka Burabusko irin dahuwar zamani.
Kayan hadi
– Garin kwaki
– Naman kaza
– Tumatir
– Albasa
– Tattasai
– Attarugu
– Koren tattasai
– Tafarnuwa
– Garin citta
– Bota
– Magi
– Man gyada
– Ruwa
Yadda ake hadawa
– A wanke naman kaza a yayyanka shi kanana.
– A markada tafarnuwa da attarugu, a zuba a cikin sai a kwaba sosai.
– A dora tukunya a wuta sai a zuba bota da man gyada kadan.
– Idan ta yi zafi sai a zuba markaden attarugu da tafarnuwa a soya sai a zuba naman kazan ana juyawa har sai ya soyu sosai.
– A zuba yankkaken koren tattasai da albasa da tumatir da ganyen albasa sai a juya sosai.
– A saukar daga wuta a ajiye a jefe.
– Sai a zuba garin kwaki a roba daban, sai a zuba ruwa kadan a jujjuya shi sosai kar ya hadu.
– A zuba hadin kazan a ciki sai a juya sosai.
– A barbada garin citta a juye sosai.
Shi ke nan sai ci!