A wannan mako zan yi rubutu ne a kan matan da sukan yi amfani da damarsu ta zuwa makaratun kwana ko jami’a wajen aikata abin da suke so. A hakikanin gaskiya ilimi sinadari ne na zaman duniya da in mutun ba ya da shi, ake ganinsa kamar dabba.
Na yi nazari a kan yadda mata suke lalata a makarantu, irin wannan lalata ita ce ke sa iyaye da dama hana yaransu zuwa makarantu. Amma duk da irin wadannan abubuwa, akwai mata nagari da duk abin da yake faruwa ba zai hana a hana su zuwa makaranta ba.
Akwai matsala biyu da nake son tattaunawa a kai. Ta farko ita ce matsalar matan aure, ta biyu kuma mata marasa aure. Amma yanzu zan mai da hankali ne a kan matan aure.
A hakikanin gaskiya idan mutum ya tsinci kansa a makaranta ko wurin aiki zai ga abubuwan al’ajabi a wurin mata. Matan aure sukan kulla alaka da maza a makarantu da sunan ’yan aji amma a gaskiya ba haka abin yake ba. Matan aure sukan kulla alaka da kawaye wadanda sukan koya masu halayen banza. Halin farko da sukan tsinci kansu a ciki shi ne maganar madigo. A kasarmu madigo laifi ne kari a kan cewa manyan addinanmu biyu ba su yarda da yin hakan ba. Akwai dalilai da dama da suke sa su fadawa irin wadannan abubuwa. Daga ciki akwai na samun abubuwan duniya kamar gida, kudi da mota. Wadansu kuma sukan yi haka ne saboda su nuna sun waye. Na biyu shi ne bin maza wajen ‘more rayuwa’ ko in ce ‘karuwanci’. Karuwanci ba abu ba ne mai kyau ballantana a ce ga matar aure. A addinin Musulunci idan mace mai aure ta yi zina to fa hukuncinta kisa ne ta hanyar jifa. Kun ga ko wannan ba karamin abu ba ne. Irin wadannan mata ba ma sa tsayawa karatun a wasu lokuta, domin yau suna Abuja gobe kuma Dubai da sauransu, haka kawai za ka ga suna yawo. Macen da ba ta da atamfar Naira dubu daya da farko, sai ka ga har gwal take sawa a makaranta. Irin matan za ka ga cewa daga karshe ma raba auren ake yi saboda mazansu na aure ba za su iya musu abin da suke so ba. Sai kuma biye wa dalibai maza a makaranta. A nan za a ga sukan mai da kansu kamar ba matan aure ba. Daga shigarsu ko mu’amalarsu ba za a iya gane matar aure ce ko ba haka ba. Wadansu matan ma har za ka ga samari suke yi a makaranta, suna ta mu’amala kamar ba matan aure ba. Irin wannan hadakar ba aba ce mai kyau da matan aure ya kamata su rika yi ba.
A karshe ina ba matan aure masu daya daga cikin wadannan halaye shawara cewa su ji tsoron Allah su daina. Domin wannan abin ya janyo wa wadansu matan matsala. Ba matan aure ba kawai har da wadanda ba su yi aure ba.
Wannan matsalar ta jawo iyaye da maza suke tsoron barin ’ya’yansu mata zuwa karatu matukar za su bar gida. Irin wadannan matsaloli sun raba aure da dama kuma sun sa iyaye sun rasa iko da ’ya’yansu sannan sun sanya iyaye jin kunya a kan abubuwan da ’ya’yansu suke yi.
Da fata za mu gyara halayenmu, kuma za mu tuna cewa duk abin da muka yi ’ya’yanmu suna kallo kuma za su so su kwaikwayi abin da muke yi. Allah muke roko Ya shiryar da mu.
Aliyu Khalid, Kaduna 08038597907