Kasancewar kuraje daga cikin ababen masu bata fuska, ya sa yake da kyau mu rika kula da fatar fuskarmu.
Kula da fatar fuska na da matukar amfani musamman ma a lokacin damina inda fuska kan yi kuraje.
- Ababen da ake bukata:
- Kwai guda daya
- Takardar ’tissue’ guda daya
- Yadda ake yi:
- A fasa kwan a cire gwaiduwar.
- A kaɗa farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa.
- A shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.
- A lullube fuskar musamman daga kan hanci har zuwa kumatu da dan ’tissue paper’.
- Idan ya bushe sai a wanke fuskar.
- Sannan sai a shafa gwaiduwar kwan a fuska na tsawon mintoci 15.
- Daga nan sai a wanke fuskar.
- Amfanin kwai ga fuska:
- Kariya daga kuraje
- Kara hasken fuska
- Rage maikon fuska
Yadda ake amfani da kwai wajen gyran kurajen fuska ke nan.
Da fatanz a gwada a gani.