✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi mummunan hatsarin mota da dare a Abuja

Mota kirar SUV da ta taho a sukwane ta makale a karkashin wata babbar mota da ke tafiya.

Wani mutum ya rasu a sakamakon hadarin mota da ya yi da tsakar dare, inda motarsa ta shige karkashin wata babbar mota a Abuja.

Hatsarin ya faru ne a daren Talata inda motar mutumin kirar SUV ta shige karkashin babbar motar da ke tafiya a kan babban titin Kubwa da ke Abuja.

Wani dan sanda da ya shaida abin da ya faru ya ce nan take mutumin, wanda shi kadai ne a cikin motar ya ce ga garinku nan.

“Yana gudu ne sosai, a lokacin ni ina daga can wurin ina wa wasu mata  kwatancen inda suke nema, sai muka ji kara, muna waigawa sai muka ga motar tasa ta shige karkashin babbar motar da ke tafiya.”

“An dauke gawar mamacin an sa ta a cikin wata motar daukar marasa lafiya,” inji shi.