✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi kuskuren harbin wani mutum a Zariya

Ba da niyya ya yi ba domin kuwa lamarin ba wani abu ba ne face tsautsayi.

Wani ma’aikacin Karamar Hukumar Zariya ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wani dan sandan kwantar da tarzoma ya harbe shi a bisa kuskure.

Lamarin dai ya faru ne da Yammacin ranar Litinin a harabar Ma’aikatar Karamar Hukumar Zariya a cewar Malam Isiyaku wanda tsautsayin ya auku a kansa.

Malam Isiyaku wanda ya ke kwance a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, ya ce ya je daukar motarsa ne daga cikin harabar ma’aikatar zai fita, sai ya ji harbin bindiga.

“Nan take na fadi kasa, ashe harsashi ya same a cinyoyina.

“Karar harbin ce ta sa Shugaban Karamar Hukumar Injiniya Aliyu Umar Idris ya fito a firgice tare da sauran jama’a.

“Nan da nan kuma Shugaban Karamar Hukumar wanda ake yi wa inkiya da Magani Sai da gwaji,  ya bayar da umarnin a hanzarta kai ni asibiti,” in ji Malam Isiyaku.

A ranar Talata Likitoci suka yi masa tiyata kuma aka yi aikin cikin nasara.

“Abin ya zo da sauki saboda harsashin ya fita duk da cewar ya sami duka cinyoyina biyu ne.”

A nasa bangaren, dan sandan da ya yi harbin ya ce ba da niyya ya yi ba ­“domin kuwa lamarin ba wani abu ba ne face tsautsayi.

“Domin bindigar ta zo faduwa ne sai na yi kokarin riketa, kawai sai ta tashi, shi ne da harsashin ya fita ya same shi,” in ji Dan sandan wanda ba a bayyana sunnansa ba.

Rahotanni sun ce bayan faruwar lamarin ne wasu jami’an ’yan sanda suka zo suka tasa keyar dan sandan zuwa ofishinsu.

Kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandar Jihar Kaduna Muhammad Jalige kan lamarin ya ci tura, domin kuwa bai amsa kirar wayar da ya yi masa ba.