✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar mutane 86 bayan fashewar tankar mai a Dikko Junction

An yi jana'izar mutane 86, wasu 43 na kwance a asibiti bayan fashewar tankar man fetur a Dikko Junction da ke kan babban titin Kaduna…

An yi jana’izar mutum 86 da suka rasu sakamakon hatsarin tankar mai da ta yi bindiga a Mahaɗar Dikko da ke Jihar Neja.

Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Abba-Ara, ya ce an gudanar da jana’izar tare da binne mutanen a kabari guda ne daga yammaci har zuwa tsakar daren ranar Lahadi.

Abdullahi bayyana cewa duk da cewa an binne yawancinsu a kabari guda, an mika gawar mutum biyar ga iyalansu domin yi musu jana’iza a garuruwansu.

Wani mutum guda kuma ya rasu a Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko da ke Ƙaramar Hukumar Gurara.

An gudanar da aikin jana’izar ne da hadin gwiwa hukumar fa masu aikin ceto da kuma hukumar lafiya a matakin farko ta jihar.

Ya bayyana cewa karin mutum 43 da suka samu raunuka sakamakon fashewar tankar man suna samun kulawa a asibiti; a yayin da iyalai da al’ummar yankin ke jimami.

Gobarar da ta tashin bayan hatsarin motar man ta koma Ababen hawa da shaguna da dama da ke kusa da wurin da ke Karamar Hukumar Gurara ta Jihar Neja.

Wannan ibtila’i ya faru ne baya faɗuwar wata tanka da ta ɗauko man fetur a Mahaɗar Dikko Junction da ke tsakanin jihar Neja da Jihar Kaduna, inda man da ta ɗauko ya tsiyaye.

A yayin da ake aikin cewa, wasu mutane suka riƙa ƙoƙari ɗibar man da ke zuba.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa jami’an tsaro sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen hana mutanan amm, jama’a suka ki. Matashin mai suna Yarima, ya ce “da ɗan sanda ya nemi hana wani matashi ɗibar man sai matashin ya xari wuƙa ya daɓa masa.”

A yayin da ake wasoson diɓar man da ke tsiyaya ne wuta ta tashi, inda a ritsa da su da kuma masu aikin ceto.

Wasu daga cikin mutane da suka rasu sum yi mummunar ƙonewar da ba za a iya gane su ba.

Wutar ta kuma kama ’yan kallo da matafiya da ababen hawa da shaguna da wuraren kasuwanci da ke kusa da wurin.

Wannan na faruwa ne watanni kaɗan bayan makamancinsa da ya faru a Ƙaramar Hukumar Taura ta Jihar Jigawa, inda kusan mutum 200 suka rasu.