Wasu mutum uku sun sha da kyar bayan jirgin kasa ya kade motarsu a yankin Iju na Jihar Legas a safiyar Litinin.
Jirgin kasan ya kade tirelar da ke dauke da kayan abincin dabbobi ne a lokacin da dirwban motar ya yi kokarin tsallake layin dogo bayan an tsayar da shi saboda zuwan jirgin, kafin ya gama wucewa kumaa jirgin ya iso inda motar take bugi bayanta.
- Yadda za ku yi rajistar neman aikin sojan kasa a Najeriya
- Rikicin Hausawa da Yarabawa: An kashe mutum 20 wasu 5,000 na gudun hijira
Jirgin kasan ya kuma kade wasu bauta masu kafa uku da ke ajiye a gefen layin dogo a unguwar ta Iju.
Mukaddashin Babban Jami’in Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kas (NEMA) a Jihar Legas, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da aukuwar hatsarin amma ya ce ba a samu asarar rai ba.
Farinloye ya ce bayan aukuwar lamarin da misalin karfe 3 na dare, jami’an hukumar NEMA da takwararta ta Jihar Legas (LASEMA), da ‘yan sanda da kuma ‘yan kwana-kwana sun dauke baburan da kuma motar da jirgin ya kade kuma tuni jirgin wanda ke hanyarsa ta zuwa Jihar Ogun ya wuce.