✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi addu’o’in neman zaman lafiya a Katsina  

A safiyar Asabar nan ce aka gudanar da addu’o’in neman samun zaman lafiya a cikin Jihar Katsina da kasa baki daya. Taron addu’o’in wadanda aka…

A safiyar Asabar nan ce aka gudanar da addu’o’in neman samun zaman lafiya a cikin Jihar Katsina da kasa baki daya.

Taron addu’o’in wadanda aka yi a cikin babban masallacin Juma’a na kofar Soro da ke cikin garin na Katsina karkashin jagorancin Babban Limamin masallacin Juma’ar Liman Mustafa Gambo, ya samu halartar manyan malamai daga sassa da bangarori daban-daban a cikin jihar.

Kamar yadda Babban Limamin ya ce, wannan taron addu’o’in na da nufin nemarwa al’umma, jihar da kasa baki daya zaman lafiya daga irin fitintinun da ke shigowa na yau da kullum.

Da yake tunasar da jama’a akan irin halin da jahar Katsina take ciki akan abin da ya shafi tsaron, Mai bai wa gwamnan jihar shawara akan wayar da kan jama’a wanda kuma shi ne wanda ya shirya wannan taron addu’o’i Alhaji Abdu Aziz Mai Turaka ya ce, “A lokacin da muke zagayen neman sasanci tare da Mai girma gwamna, akwai wata yarinya wadda bata wuce shekaru 10 zuwa 12 ba, wadda ta fada hannun masu satar mutane da yin garkuwa da su, ta ce, kullum sai an yi amfani da ita fiye da biyu ko uku. Haka ma sauran matan da suke hannunsu abin yake.”

Alhaji Abdu Aziz, ya yi dogon bayani mai motsa zuciya akan irin halin da rashin tsaron ke haifarwa. Akan haka ne ya ce, lallai sai al’umma sun tashi tsaye akan yin addu’o’in neman zaman lafiya domin taimakawa gwamnati akan irin qoqarin da take yi.

Wani sashe na masu yin addu’o’in a cikin babban masallacin Juma’a na Kofar Soro a Katsina

Shi kuwa Malam Isma’ila Zakariyya Alkashnawi, daya daga cikin malaman da suka yi addu’o’in, ya ja hankalin malamai ne akan irin yadda suka yi biris da batun yin wa’azoji a wurare daban-daban don aza mutane a hanya.”