Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa na Kaduna reshen kasuwar Shaikh Abubakar Gumi Alhaji Ibrahim Shehu Daudawa ya ce sun shirya tsaf domin a bude kasuwar.
Aminiya ta samu labarin cewa hukumar kula da kasuwannin jihar na shirin bude kasuwar Shaikh Abubakar Gumi a ranar Juma’a bayan kusan watanni shida da rufewa saboda cutar coronavirus.
Shugaban ‘yan kasuwar wanda Aminiya ta zanta da shi ya ce ‘yan kasuwar sun shirya domin ganin an bude ta saboda ci gaba da harkokinsu.
Ya ce ba Kasuwar Shaikh Gumi kadai ba har da kasuwanni da ke zagaye da ita kamar Checheniya da Kantin Kwari duk an fara shirin bude su.
Ya kara da cewa a makon jiya ne suka zauna da hukumar kula da kasuwannin inda ta ba su wasu sharudda kafin a bude kasuwannin.
“Sun ce mu tabbatar da cewa akwai tazara tsakanin masu saye da masu sayarwa sannan kowane mai shago ya samar da abun wanke hannu.
“Sannan kofofin kasuwar 29 manya da kanana dole a samar da ruwa da sabulu domin duk wanda zai shiga ciki ya wanke hannunsa.
“…kuma duk wanda zai shiga sai ya sanya takunkumi.
“Duk mun yi wannan domin mun kammala sannan muka kira su shugabannin domin su gani.
“Har da na’urar auna zafin jiki mun saya da kuma durom-durom na zuba ruwa sannan mun samar da takunkumi dubu biyu su kuma sun yi alkawari ba mu kusan dubu goma.
“Sannan mun tabbatar da cewa za mu rika zagayawa cikin kasuwa domin ganin ana bin doka da oda. Kasan ba a son cunkoso a shago da layukan cikin kasuwa.
“Akwai kofofin shiga cikin kasuwa wadanda za mu mayar da su na shiga ne kawai, duk wanda ya shiga ba zai dawo ta wajen ba domin kauce wa cunkoso a bakin hanyar shiga.
“Yanzu cikin kasuwar ana feshin kwari domin duk akwai ciyayi ciki.
“Sun ce idan ba a kammala shara da gyarar ba za a jinkirta bude kasuwar zuwa ranar Juma’ar nan. Mu dai a shirye muke a bude kasuwar”, inji shi.
Game da ko za su kammala aikin sharar kafin lokaci sai ya ce, “Kamar kasuwar Shaikh Gumi ana iya kammala ayyukan a kan lokaci, amma sauran kasuwannin da ke kewaye kamar su Checheniya a yanzu haka akwai inda za ka samu ciyayi sun yi tsawo wanda kafin a kammala cire su yana iya daukar lokaci.
“A yanzu aikinsu an fara amma ba a kammala cire ciyayin ba ballantana a fara shara”, inji shi.
Game da ko su ke daukar nauyin feshin ciyayin sai ya ce, “Nan cikin Kasuwar Shaikh Gumi gwamnati ke yi amma na cikin Checheniya jama’ar kasuwane da kuma kamfanin da gwamnati ta bayar zai rika share kasuwa”, inji shi.