A kwanakin baya ne bidiyon wata mata da ’ya’yanta biyu da makwabciyarta ta mayar da su Kiristoci ya karade kafofin sada zumunta.
Aminiya ta zanta da matar mai suna A’isha Muhammad wacce a yanzu take zaune a garin Sabo a Jihar Ondo, kan lamarin.
- Najeriya ta fitar da kayan Dala 1.9 zuwa Amurka a 2020
- NAJERIYA A YAU: Halin da ’yan gudun hijirar Bama ke ciki bayan komawa garinsu
A’isha ta ce bayan mijinta ya rasu a lokacin suna zaune a Ado Ekiti a Jihar Ekiti, sai rashin lafiya ta same ta.
“Ganin mawuyacin halin da ta shiga sai makwabciyar wacce asalinta Musulma ce mai suna Kudirat, amma mijin da ta aura ya mayar da ita Kirista, ta nemi in bar mata ’ya’yan domin ta ba su kulawa.
“Sai na bar su na tafi gida Arewa domin jinya, amma ina kiran ta a waya muna gaisawa, sai ta ce min ’ya’yana suna nan lafiya,” inji ta.
A’isha Muhammad ta ce, bayan wani lokaci sai ta daina samun matar a waya, bayan ta samu sauki ta dawo gidan da suke zaune da ita, amma aka ce mata ta koma Legas da zama kuma ta tafi da yaran.
“Haka na bazama nema, kuma malamai suna mini addu’a har yaran suka kai shekara biyar a wajenta.
“Sai lokacin Allah Ya kaddara wata mata makwabciyarmu ta ce ta samu lambarta. Da ta kira ta fada mata ga uwar yaran nan, sai ta rufe matar da fada, ta yanke waya.
“To a wannan lokaci matar ta ce an ce tana zaune ne a Ikorodu.
“A haka na nemi kudi na koma Legas na je unguwar na nemi dan acava yana ta zagawa da ni unguwa-unguwa.
“Kwatsam sai na ji muryar karamar ’yata ’yar shekarar tara mai suna Zainab tana kiran sunana.
“Ko da na gan ta na ce ina ’yar uwarta sai ta ce tana gidan wata mata mai sayar da abinci, ba a gida guda suke ba.
“Muka je in taho da ita, amma sai matar da ke rikon ta, ta ki yarda,” inji ta.
Ta ce, daga baya ta samu ’ya’yanta bayan Sarkin Hausawan yankin ya shiga maganar, kuma sun ba ta ’ya’yan ne ba da don suna so ba, “Domin sun sauya masu suna daga Zainab zuwa Sarah, dayar kuma daga Rukayya zuwa Debora, dayarsu ma da kuros a wuyanta na same ta.
“Yanzu haka na sa ana yi musu addu’a, domin na same su ba yadda suke ba. Suna bukatar addu’a, kuma ina da rauni ba ni da karfi, ba ni da sana’a, yaran kuma sun zama marayu, yanzu haka aikatau nake yi a garin Sabo Ondo domin na samu abin da zan kula da su,” inji ta.
Aminiya ta tuntuvi Sarkin Hausawan Adamo Olorunda da ke yankin Ikorodu a Legas, inda lamarin ya auku, Malam Abdurahman Sulaiman inda ya ce, a lokacin da matar ta samu ikon kwato ’ya daya daga cikin ’ya’yan, sai suka hana ta daya ’yar.
“Bayan ta zo da maganar ce na sanar da ’yan sanda domin na san abu ne da ya kamata hukuma ta shiga ciki.
“Nan muka shigar da maganar a ofishin ’yan sanda na Adamo Olorunda, amma abin ya ba mu mamaki domin ’yan sanda ba su dauki wani mataki ba, sai suka bar ni da maganar.
“Lokacin ainihin wadda ta dauko yaran ta tafi Arewa sayo doya, sai suka ce a bari ta dawo.
“Ko da ta dawo ta so ta yi gardama a kan yaran sai na nuna mata mun shigar da maganar wajen ’yan sanda, don haka zan kira ’yan sanda.
“Da ta fahimci haka sai ta saduda, nan take na kira ’yan sanda su ba mu iko mu zo wajensu a rubuta takardar yarjejeniya, amma sai suka ki.
“Suka ce ai in dai matar ta ba da yaran magana ta kare, suka ce ni ma zan iya jagorantar rubuta takardar.
“Haka na sa sakatare ya rubuta takarda, matar da ta dauko yaran ta sa hannu, ita ma mahaifiyar yaran ta sanya hannu,” inji shi.
Abubakar Alhassan shi ne Sakataren Sarkin Hausawan, kuma shi ya nadi bidiyon matar da ya karade kafafen sadarwa, ya ce, bayan ya yada bidiyon sai aka rufe shafinsa a Facebook.