’Yan Arewa mazauna kudancin Najeriya musamman jihohin Abiya da Imo da Ribas da Legas da Ogun wadanda tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar #EndSARS ta rutsa da su, sun ce sun samu kansu a cikin mawuyacin hali a makon jiya.
A jihohin Abiya da Legas ne ’yan Arewar suka fi haduwa da bala’in asarar dukiya da rayuka kamar yadda Aminiya ta samu bayani.
- Zanga-zangar #EndSARS: Matasan arewa sun bukaci a kai zuciya nesa
- Yadda masu zanga-zanga suka kai hari gidan sanatoci
An kashe ’yan Arewa takwas a Ribas
Mutum takwas mazauna kusa da birnin Fatakwal a Jihar Ribas ne al’ummar Arewa mazauna yankin suka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon harin da masu zanga-zangar #EndSARS suka kai musu.
Daya daga cikin shugabannin ’yan Arewa mazauna jihar Alhaji Musa Sa’idu ne ya tabbatar wa Aminiya haka, inda ya ce “Mutum takwas ne zauna-gari-banza suka kashe su, wadansu ma an sare musu kai kafin a jefar da gawarwakinsu a gefen titi, ’yan Arewar ne suka rika tsinto gawarwakin.”
Alhaji Musa Sa’idu ya ce, “Yanzu haka daruruwan ’yan Arewa na zaman gudun hijira a birnin Fatakwal, muna dafa abinci muna kai musu.”
Aminiya ta samu labarin cewa a farkon zanga-zangar an kona motocin ’yan Arewa da suka kai kayan abinci da dabbobi lamarin da ya jefa al’ummar cikin firgici.
Wani mazaunin Fatakwal Malam Saminu Bello, ya ce “Muna zaman kunci da rashin walwala.
“Babu yadda za mu fita ko neman abinci ko gudanar da sana’o’inmu, babu wata hobbasa da gwamnati ke yi don magance mana matsalar.”
Shi kuwa Garba Idris cewa ya yi suna fita harkokin kasuwanci a cikin garin Fatakwal za su fuskanci wulakanci da cin zarafi daga ’yan asalin jihar wadanda suke nuna musu cewa can ba Arewa ba ce.
Yawancin wadanda Aminiya ta ji ta bakinsu sun ce wulakanci ya yi yawa musamman ganin babu wani matakin da shugabannin yankin ke dauka don magance lamarin.
An kashe mutum 6 an kone motocin ’yan Arewa 41 a Aba
’Yan Arewa da ke harkokin kasuwanci a Kasuwar Albasa ta garin Aba a Jihar Abiya sun ce an kashe musu mutum 6 kuma an kone musu motoci 41 ciki har da tireloli 29.
Shugaban Kasuwar Albasa ta Aba, Alhaji Salisu Danwanzam ne ya shaida wa Aminiya haka, inda ya ce mutum uku da aka kashe a Kasuwar Albasa ta Aba sun hada da Abdullahi Kaura daga Jihar Kano da Kasimsu Aleiro daga Kebbi da Isa Musa daga Taraba.
Sai mutum uku da bai gano sunansu ba da aka kashe a Kasuwar Kankana ta Aba.
Alhaji Salisu Danwanzam ya ce an kone tireloli 29 daga cikin 50 da suke kasuwar kuma an kone kananan motoci 12 na ’yan Arewa da suka boye su a kasuwar.
Alhaji Salisu Danwanzam ya ce, “Motocin mutanenmu 41 suka kone, mun boye motoci 50, sun kone tireloli 29 da kananan motoci 12 na ’yan Arewa da suka kawo mana kaya.”
Wani mazaunin garin Aba, Alhaji Sa’idu Bala ya shaida wa Aminiya cewa: “Ban taba ganin masifa irin ta wannan rana ba, matasan nan masu zanga-zangar #EndSARS da suka tunkaro kasuwarmu, sai jami’an tsaro suka gudu suka bar mu da su.
Su kuma suka hau sarar mu da adduna suka sace mana dukiya.”
Balarabe Kabir ya ce, “Matasan wadansu sun zo dauke da manyan bindigogi suka rika harbi, mu kuma muka nemi hanyar tsira da rayukanmu.
“Gaskiya babu wani taimako da jami’an tsaro suka yi mana.”
Dan uwan marigayi Kasimu Aliero mai suna Abdullahi Danmaske ya ce “Marigayin daga garin Aleiro a Jihar Kebbi ya fito, saurayi ko auren fari bai yi ba.
“Yana tsaye a jikin wata tirela harbin da masu zanga-zangar suka yi ne sai harsashi ya same shi, ya yi ajalinsa.”
Shi kuwa dan uwan marigayi Abdullahi Kaura mai suna Bilyaminu Sauke cewa ya yi “Marigayi na da mata 4 da ’ya’ya 8, korar da aka yi ana harbe-harbe garin ya gudu ne sai harsashi ya same shi.
“Ya fito ne daga Karamar Hukumar Karaye a Jihar Kano.
‘Mun yi asarar sama da N5bn a Aba’
Alhaji Salisu Danwanzam ya ce asarar da suka yi za ta kai ta sama da Naira biliyan bakwai.
Ya ce an kone musu motoci 9 da kowace dauke da buhun albasa 270, sannan an kone shaguna 103 a sashin masu sayar da shinkafa da wake, sai masu kayan tireda wadanda suka yi asarar kimanin Naira biliyan biyu.
“Mu kuma ta Naira biliyan biyar ka ga Naira biliyan bakwai ke nan”, inji shi.
A Jihar Imo ’yan Arewa 26 da ke harkokin kasuwanci a Kasuwar Albasa ta garin Orlu aka kwashe zuwa garin Owerri fadar jihar, bayan da masu zanga-zangar #EndSARS suka far musu.
Kanen Sarkin Hausawan Owerri, Alhaji Sulaiman Ibrahim Sulaiman ne ya shaida wa Aminiya haka.
Ya ce Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya ba iyalan wadanda masu zanga-zangar #EndSARS suka kashe tallafin Naira dubu 500 a Kasuwar Albasa ta Orlu da ke Jjihar Imo.
Alhaji Suleiman Ibrahim Suleiman ya ce “Gwamnan ya ba iyalan mamaci na biyu da aka kashe Naira dubu 500 su ci abinci.”
Ya ce “Mutum biyu aka kashe a kasuwar albasar, mutum na farko harbinsa masu zanga-zangar suka yi aka kai shi asibiti.
“Shi kuma mutum na biyu direba ne da ya kawo wake sai masu zanga-zangar suka daka masa wasoso suna dibar waken a mota, sai ya ce su bari ya isa haka, ya shiga motar zai ja ya tafi sai wani cikin masu zangazangar ya cire bindiga ya harbe shi ya mutu nan take,” injishi Alhaji Suleiman Ibrahim.
Ya ce mutum na farko da aka kashe bai sani ba ko yana da iyali, amma na biyu direban da ya kawo wake daga Arewa zuwa Orlu yana da mata biyu da ’ya’ya biyu shi ne wanda Gwamna ya ba da Naira dubu 500 su ci abinci. “Na yi magana da iyalansa ta waya”, inji shi.
Ya ce a ranar Juma’ar da ta gabata ya je garin Orlu ya kwaso mutum 26 zuwa Owerri don mayar da su zuwa garuruwansu na asali, kuma suna cikin koshin lafiya.
Ya ce Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ya ba shi kudi ya bai wa kowanensu Naira dubu 10 su tafi gida. Sai dai ya ce babu mota ko daya da aka kona a kasuwar kamar yadda ake yadawa a kafafen sadarwar zamani.
Amma wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an kona masallacin kasuwar.
Ba mu fuskanci barazana a Kalaba ba
Masu zanga-zangar #EndSARS a Kalaba fadar Jihar Kuros Riba sun shafe tsawon wunin Juma’ar makon jiya suna fasa shaguna da rumbunan ajiye kayan abinci na gwamnati.
Lamarin ya jefa birnin Kalaba a cikin firgici ganin an kai daren Asabar ana musayar wuta a tsakanin masu zanga-zangar wanda ya kai ga kafa dokar takaita zirga-zirga a jihar.
Hausawa mazauna Kalaba sun shaida wa Aminiya cewa babu wata barazana ko hari da aka kai musu yayin zanga-zangar da aka shafe kwana uku ana yi a Kalaba da sauran sassan jihar.
Sun ce an dauki matakan tsaro a Layin Bagobiri, Unguwar Hausawa inda aka tura sojoji saboda kada masu zanga-zangar su kai musu hari.
Daya daga cikin ’yan Arewa mazauna Kalaba, Muhammad Aminu ya shaida wa Aminiya cewa “Ba a kai mana hari ba, sai dai mun yi zaman kunci ba fita neman abinci.
“Da zanga zanga-zangar ta yi kamari ne aka shiga sace-sacen kayan abinci da barna sai gwamnatin jihar ta kafa dokar takaita zirga-zirga daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe inda daga bisani a rage ta zuwa karfe 4:00 na yamma zuwa 8:00 na safe”.
Salamatu Bello ta bayyana yadda suka yi zaman dardar ne a jihar, “Mun wahala abin da za mu ci ya yi mana wahala mun kasance a kulle, abin da jama’a za su ci ne babban kalubalen mutane,” inji ta.
Wata mai sayar da abinci A’isha Abdallah ta shaida wa Aminiya cewa “Sojoji sun fatattake ni na koma gida, na yi asarar abincin sayarwar da na kawo.”
Mun shiga halin ha’ula’i a Legsa –Dansudu
Daya daga cikin shugabannin ’yan Arewa mazauna Legas, Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu ya shaida wa Aminiya cewa ’yan Arewa mazauna Legas sun shiga halin ha’ula’i lokacin tarzomar inda aka yi ta kai musu farmaki don jawo su cikin rikicin.
“A wurare da dama an yi ta kai mana hari don a jawo mu cikin rikicin amma mu shugabanni muka yi ta fadakar da jama’armu illar shiga tarzomar, muka kwantar da hankalinsu, kuma alhamdulillahi mutanenmu sun ji kiran ba su shiga yamutsin ba”.
‘An kashe mana mutum 25 a Legas’
Alhaji Shuaibu Dansudu ya ce: Sai dai abin takaici a wasu wuraren an kai wa mutanenmu hari an kone musu dukiyoyinsu.
A yankin Fagba da ke Karamar Hukumar Ifako Ijaye a Jihar Legas lamarin ya fi muni domin an kashe mana akalla mutum 25.
Ya ce a yankin Abbatuwa ta Agege da ke Oko-Oba a Karamar Hukumar Ifako Ijaye an kone manyan motocin dakon dabbobi da dama, an sace shanu da awaki, Sai dai daga baya ana bin wadanda suka sace shanun ana karba ana ba su tukwicin Naira dubu 20 zuwa 30, suna dawowa da su.
“Amma wadanda suka sace awaki da raguna da tumaki ba su dawo da su, inji shi.
Ya ce farmakin da aka kai wa yan Arewa a Abbatuwa, matasa yan Arewa sun nemi daukar fansa, amma shugabanninsu suka hana.
Sarkin Fulanin Kasuwar Abbatuwa, Alhaji Muhammadu Dan-Mubaffa kuwa ya kira taron gaggawa ne bayan masu zanga zangar #EndSARS sun kai hari ga direbobin motocin shanu, inda ya bukaci yan Arewa su kai zuciya nesa.
Sarkin Fulanin wanda ya kira taron ne a ranar 21 ga Oktoba bayan farmakin da aka kai wa direbobi da yaransu a Fagba, ranar Talata, lamarin da ya jawo salwantar rayuka da dama.
Shugaban Matasa Yan Kasuwar Shanu ta Abbatuwa, Alhaji Muhammadu Tom, ya shaida wa Aminiya cewa zuwa safiyar Laraba 21 ga Oktoba sun tattaro gawarwakin direbobin manyan motocin shanu da na yaransu su takwas, wadansu an kone su kurmus yayin da wadansu aka yi musu mummunan raunuka.
Mun karbo takarda daga wurin yan sanda, mun yi musu sutura a makabartar Agege.
Akwai wadanda aka gane yan uwansu akwai wadanda aka kone su kurmus.
Akwai wani Bazabarme da aka kashe, yan uwansa sun karbi gawarsa sun binne, sai wani dan ga-ruwa dattijo da aka kashe shi da matarsa mun gano gawarsu a dakinsa, amma gawarwakin wadanda aka kone ba mu taba su ba.
Kuma an kone manyan motocin shanu biyu da tanka daya an kuma farfasa bakwai, inji shi.
Ya ce da farko yan Arewa mazauna Unguwar Fagba sun kwashe iyalansu sun kai Agege, amma daga baya shugabanin Yarbawa suka nemi su dawo da su, kuma shugabanin Yarbawan da matasansu da na yan Arewa suka hadu suka bai wa unguwar tsaro.
Dama batagari ke kawo harin da yan unguwa suka hada kai sai rikicin ya lafa, inji shi.
A yankin Ajegunle da Apapa a Karamar Hukumar Ajeromi Ifelodun da batagari suka fara kone sakatariyarta, Hausawan yankin sun kasance cikin dardar.
Malam Musa Nayis, Mai ba Shugaban Karamar Hukumar Shawara ta Musamman, ya shaida wa Aminiya cewa, hankalin jamaa ya tashi, Ganin yadda zanga-zangar ta rikide tarzoma, abu ne mai wahala mutum ya samu natsuwa.
“Jamaa sun ci gaba da zaman dardar saboda tsageru na kone kadarorin gwamnati da na jamaa.
“Abin da za mu ce Allah Ya kare aukuwar haka nan gaba, Ya jikan wadanda aka rasa, wadanda suka yi asara Ya mayar musu da mafi alheri, inji shi.
Yadda aka kashe mana dangi
Muhammad Nasiru dan uwan Ibrahim Dodo ne daya daga cikin matasan da aka kashe a tarzomar Fagba, ya shaida wa Aminiya cewa matashin dan asalin Banki a Jihar Borno, yana sanaar acaba ce a Legas, kuma yana bakin sanaarsa ce lamarin ya rutsa da shi.
Gida guda nake da mahaifansa a Banki a Jihar Borno, a gabana ya taso, sannan da na fara zuwa Legas ya zo, muna nan tare yana acaba, yanzu haka iyayensa sun koma Mubi a Jihar Adamawa.
“An kashe shi ne lokacin da ya fita sanaa da babur dinsa, shi da wani abokin sanaarsa, ban san sunansa ba, amma dukkansu biyun an kashe.
Wadanda abin ya faru a idonsu sun ce an biyo Ibrahim ne da ya fadi aka sassara shi, daga nan suka dauke shi suka kai mahadar Fagba suka sa taya suka kone, ba mu samu yi masa sutura ba saboda sun kone shi kurmus shi da abokin sanaarsa.
“Babu abin da ya rage a jikinsu da za mu kai makabarta mu binne, wadanda suka kona haka kawai.
“Akalla sun kai mutum bakwai ciki har da wata mace da danta a goye, inji shi.
Malam Usman Musa wanda ya rasa kaninsa Mustafa Muhammad Musa ya shaida wa Aminiya cewa, dan uwansa ya gamu da ajalinsa ne lokacin da yake fitowa daga garin Algbado da ke Jihar Ogun inda ya shiga Unguwar Fagba rikicin ya rutsa da shi batagarin suka sassare shi a ranar Alhamis din makon jiya.
Da bayani ya iske mu mun yi saurin isa wajen, muka iske sun kashe shi amma ba su kai ga kone gawarsa ba, nan muka dauko shi aka yi masa sutura a makabartar Agege.
“Mustafa ya rasu ya bar yaya uku da matar aure a Unguwar Aisami a Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano, mahauci ne da ke aiki a nan mayankar Kasuwar Abbatuwa, inji shi.
Bashir Abba wanda ya rasa dan uwansa mai suna Mustafa Idris dan asalin Unguwar Sani Mainagge a Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, ya shaida wa Aminiya cewa suna aikin amalanke ne tare da marigayin a Kasuwar Abbatuwa ta Legas.
Ya ce an kashe dan uwansa ne lokacin da yake kokarin ceto wadansu mata da yara da rikicin Fagba ya rutsa da su.
Bayan da aka fada masa akwai wadansu mata da yara kanana da rikicin ya rutsa da su ya je ya tsallako da su.
“Daga baya ya koma ya dauko wani mutum da aka sassare shi, ko da ya rungumo mutumin yana kokarin ketarowa sai shi ma suka sare shi a wuya ya rasu.
“Mun yi masa janaiza a makabartar Agege, bai dade da dawowa daga Arewa ba, saboda matarsa da yayansa hudu na zaune ne a Kano, inji shi.
Na ga mutuwa kiri-kiri
Wani matashi dan asalin Jihar Zamfara da aka yi wa mummunan rauni mai suna Idris Abubakar, ya ce ya ga mutuwa kuru-kuru a ranar Alhamis din makon jiya bayan rikicin ya fara lafawa.
Muna zaune a gida sai aka zo aka ce mana tarzoma ta rutsa da mata da yara kanana, to muna da yan uwanmu da abokan mutunci, don haka muka fita don kwaso su.
“Na fita na ga wata matar aure hankalinta a tashe ko suturar kirki babu a jikinta, na samu zane na ba ta na riko ta ita da danta muka fito.
“Daga baya muka koma muka iske kananan yara iyayensu sun gudu sun bar su, nan na goyo wadansu a baya na rungumi daya na kamo hannun daya, ban yi aune ba sai na ganni a tsakiyar maharan.
“Nan suka hau ni da sara da na ga jini ya fara fita a jikina gudun kada a yi biyu babu, a hallaka ni a hallaka yaran sai na yi ta kaina da yaro daya ragowar ban san halin da suke ciki ba.
“Sun sassare ni a kai da gadon baya, amma alhamdullihi ina samun sauki an yi min dinki, inji shi.
Ba a taba mu a Ogun da Oyo ba amma…
Duk da ba a taba yan Arewa mazauna Jihar Ogun ba, Sarkin Hausawan Abeokuta, Alhaji Muhammad Hassan Hassan da Mai ba Gwamnan Jihar Shawara kan Alamuran Kabilu, Malam Hadi Sani sun shirya tarurrukan zaman lafiya a tsakanin Hausawa da Yarbawa, inda suka cimma matsayar ba za su yarda a yi zanga-zanga a Unguwar Hausawa da ke Sabo Abeokuta ba.
Sarkin Hausawan ya ce wannan na cikin matakan da suka dauka.
Kuma Allah Ya takaita balain, mun kasance cikin salama duk da zuciyarmu ba ta natsu ba, domin ba mu ji dadin abubuwan da suka faru a wasu jihohin ba, inji shi.
Alummar Arewa mazauna Jihar Oyo ma sun ce babu abin da ya taba rai ko dukiyarsu a tsawon mako biyu na zanga-zangar da ta rikide tarzoma a jihar.
Sarkin Hausawan Ojo, Alhaji Ali Yaro da ofishinsa ke kusa da ofishin yan sandan da aka kashe jamiansu biyu aka kone su kurmus, ya ce, masu zanga-zangar sama da dubu suka toshe manyan hanyoyi biyu kafin su dumfari ofisoshin yan sanda su cinna musu wuta.
Ya ce sun ci gaba da kone-kone kwana biyu ba tare da sun taba su ba.
Har zuwa ranar Jumaa da suka janye daga kan hanyoyi, babu wanda ya rasa ransa ko ya yi asarar dukiya daga cikin mutanensa.
Masu zanga-zangar sun kafa daba a Mokola kusa da Unguwar Sabo mazaunin Hausawan Ibadan amma har suka gama ba su taba kowa ba.
Shugaban bangaren masu wake a Kasuwar Bodija, Alhaji Garba Uwa ya ce babu wanda ya shiga kasuwar da sunan zanga-zanga.
Sai dai masu kai musu kaya daga Arewa sun dakatar, yayin da masu zuwa saye suka daina zuwa saboda tsoro.
Ka san idan babu mai saye, to dole dan kasuwa ya yi hasara, inji shi.
Shugaban Kasuwar Sasa, Alhaji Usman Yako ya ce sun yi dimbin hasara a dalilin rubewar kayan gwari.
Amma muna godiya ga Allah da Ya sa zanga-zangar ba ta shigo kasuwarmu ba, inji shi.
Sarkin Hausawan Akinyele, Alhaji Ado Sulaiman wanda jigo ne a Karar Shanu ta Akinyele ya ce babu abin da ya shafi rayuwarsu kuma suna fadakar da mutanensu kada su shiga cikin boren.
Saboda kyakkyawar dangantaka a tsakaninmu da Baale na Akinyele ya tura yan sintiri da mafarauta yankin su kare ofishin yan sanda na karar, inji shi.
Aminiya ta gano cewa wadansu kananan yan kasuwa masu talla a kai da masu tura baro zanga-zangar ta rutsa da su inda batagari suka kwace kudade da wayoyi da kayan sayarwarsu.
Rahotanni sun ce yan Arewa mazauna jihohin Osun da Ondo da Ekiti, ma zanga-zangar ba ta shafe su ba amma sun hadu da karancin harkokin kasuwanci.