Wasu matasa da ake zargi da daukar doka a hannu da ke yankin Oku a karamar hukumar Boki ta jahar Kuros Riba sun kona mutum sama da goma bisa zargin maita da hana al’ummar yankin ci gaba.
Bayanan da Aminiya ta samu daga bakin wani mazaunin kauyen ya tabbatar da faruwar hakan yace “wani babban dan siyasa ne mai rike da muqami a wannan gwamnatin yasa aka yi hakan, wasu matasa ne suka rika bi gida-gida suna fito da dattawan maza da mata suna kona su” in ji majiyar.
Daga cikin wadanda aka kona Akwai sarakunan gargajiyar yankin uku Edward Kekong da John Otu, da kuma Bernard Kekong.
Wasu daga cikin wadanda aka kona basu mutu ba amma sun yi mummunar kuna, kuma babban xan siyasar ya hana ayi musu jinya a Asibitin da ke Okundi .
Wakilin Aminiya ya tuntubi Mista Alfred Mboto babban mai ba gwamnan kuros riba shawara kan harkokin tsaro game da lamarin, sai yace “na tuntubi takwaran aikina mai kula da tsakyar jiha ya tabbatar min da hakan ya faru ya kuma bayar da umarnin a kama wadanda ake zargi da kona mutanen” in ji shi.
‘Yan sandan yankin basu yi wani katabus ba na hana aikata aika-aikar, kana ance dan siyasar ya gargadesu da su yi nesa da lamarin.
Aminiya ta tuntubi babban jami’a da ke magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Irene Ugbo game lamarin, wacce tace “Zuwa yanzu muna bin diddigin alamarin da zarar mun samu karin bayani zan sanar maka”.
Tarihi ya nuna cewa jihar Kuros Riba jiha ce da ke da tarihin kashewa tare da muzgunawa wadanda ake zargi da maita.
A baya can a jihar ana daukar tagwaye a matsayin mayu kafin daga bisani turawan mulkin mallaka su wayar wa jama’ar jihar kai bisa lamarin.