✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kama tankokin yaki a iyakar Najeriya da Kamaru

Har yanzu ana cikin rudani da rashin tabbas kan mamallakin wasu tankokin yaki masu sulke da jami’an tsaron Najeriya suka kama a Jihar Adamawa. An…

Har yanzu ana cikin rudani da rashin tabbas kan mamallakin wasu tankokin yaki masu sulke da jami’an tsaron Najeriya suka kama a Jihar Adamawa.

An kama tankokin shida ne a iyakar Najeriya da Kamaru, a iyakar Konkol da ke Karamar Hukumar Maiha a Jihar Adamawa

Wata majiya ta ce motocin yakin na gwamnatim Nijar ne, amma gwamnatin Najeriya da Kamaru duk sun ki bayar da cikakken bayani game da motocin.

Wadansu kuma sun ce motocin mallakar Kamaru ce, yayin da wasu bayanai ke cewa mallakar kasar Amurka ce.

A lokacin da labarin ya fito fili an ga Kwamandan Sojoji na Bataliya ta 23, Birgediya S.G Mohammed ya mika motocin ga Kwanturolan Kwastam mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, Olumoh Kamaldeen a kauyen Konkol. Sannan Hukumar Kwastam a Yola ta kira taron manema labarai da nufin bayyana yadda lamarin yake, amma daga baya ta fasa, inda ta ce komai ya koma Abuja.

Da Aminiya ta tuntubi Kamaldeen domin karin bayani, bai amsa kiran waya ba har lokacin hada wannan labari, amma Aminiya ta jiyo cewa Kwastam ta kaddamar da wani sabon bincike  game da lamarin.

Kakakin Hukumar Kwastam na Kasa, Mataimakin Kwanturola, Joseph Attah ya tabbatar wa Aminiya cewa Shugaban Hukumar, Kanar Hameed Ali (mai ritaya) ya ba da umarni a ci gaba da bincike.

A cewar Kakakin Hukumar, “Da gaske ne an kama motocin yaki masu sulke guda shida a Konkol na Karamar Hukumar Maiha a Jihar Adamawa. Jami’an tsaro da suka kunshi sojojin kasa da DSS da Kwastam ne suka kama tankokin. Sai aka ajiye su a wajen sojojin kafin daga baya a damka wa Kwastam. Bayanan da muka fara samu daga direbobin tankokin sun nuna cewa sun zo wucewa ta Najeriya ce, amma aka kama su saboda babu wasu takardu da ke nuna hakan domin idan za ka shige ta wata kasa, dole ka mallaki takardun izini da sauransu.”

Amma wani babban jami’in gwamnati ya fada wa Aminiya cewa Gwamnatin Amurka ce ta ba kasar Nijar kyautar tankokin, inda ya ce ko a baya Najeriya ta taba samun irin wannan kyauta daga Amurka.

Majiyar ta kara da cewa an yi duk abin da ya kamata kama daga cike takardun izini da sauransu, inda ya ce jami’an gwamnatin Amurka sun yi mamakin kama tankokin, inda ya zargi kuskuren bayar da bayani cikin sauri a tsakanin jami’an tsaron Najeriya a matsayin abin da ya jawo matsalar.”

Shi ma wani babban jami’in tsaro da yake da masaniya kan lamarin ya bayyana wa Aminiya yadda abin ya faru, inda ya ce, “Jami’an DSS ne suka gano tankokin na shigowa Najeriya, inda nan-da-nan suka sanar da hedkwatarsu a Abuja, sannan suka hada hannu da sauran jami’an tsaro wajen aikin. Da tankokin suka iso bakin iyakar Najeriya, sai muka bukaci a kawo mana takardun izini da sauran takardun shaida, amma babu.”

Wani soja da ke cikin wadanda suka rako tankokin daga kauyen Jamtari a iyakar Najeriya da Kamaru zuwa Yola ya ce tankokin Nijar za su je amma daga Amurka suke, sannan sun dan yada zango a sansanin sojojin Amurka da ke Kamaru, ya kara da cewa direbobin mutanen Najeriya ne.

Wata majiyar kuma cewa ta yi gwamatin Kamaru ce ta ba Nijar kyautar tankokin yakin kasancewar ban da sojojin hadaka na Multi National Joint Task Force (MNJF) da ke tsakanin Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya, Kamaru da Nijar suna da wata alaka ta daban, inda hakan ya sa Kamaru ta ba Nijar wadannan tankoki, “Kuma ina tabbatar maka cewa ba a karya wata doka ba,” inji majiyarmu.