’Yan sanda sun cafke wasu mutane bakwai bisa zargin fasa gidaje da kuma sata a Jihar Yobe.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, ya sanar a ranar Juma’a a Damaturu ccwa wadanda ake zargin sun kware wajen fasa gidaje.
A cewarsa, an kama su ne a sassa daban-daban na jihar bayan korafe-korafen al’umma kan fasa gidaje da sata da dangoginsu.
Ya ce, dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa, kuma ’yan sanda sun kwato wasu kayan da aka sace daga wurare daban-daban.
Ya kara da cewa an kama wasu mutane da suka sayi kadarorin da aka sace.
Dungus ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bayan an kammala bincike.
Ya ce kayayyakin da aka kwato sun hada da kayan abinci, talabijin, injinan wutar lantarki, barguna, wayoyin hannu, tukunyar gas, kafet da dai sauransu.
Ya kara da cewa, “Rundunar ta shawarci jama’a da su kula da sayen kayayyaki daga mutanen da ba a yarda da su ba,” in ji shi.
Ya kuma ba da tabbacin cewa ’yan sanda ba za su yi kasa a gwiwi ba wajen fatattakar masu aikata laifuka daga jihar tare da neman goyon bayan jama’a.