Masu zanga-zangar EndSARS a yankin Lekki Jihar Legas, sun kama tare da mika daya daga cikinsu ga ’yan sanda bisa zargin sa da satar waya.
Bayan matashin ya saci wayar wani mai zanga-zangar, ya damka ta wa abokinsa ya tsere da ita ne masu zanga-zangar suka kama shi kafin ya tsere.
- ’Yan daba sun kashe mutum uku a zanga-zangar #EndSARS
- ‘Muna neman taimakon Indiya don fitar da mutane daga talauci’
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Legas, Muyiwa Adejobi, ya tabbatar da haka sannan ya ce ana ci gaba da kokarin kamo wanda ya tsere din.
“Masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, sun kame tare da mika mana daya daga cikinsu mazaunin Ojuelegba, saboda satar waya”, inji shi.
Ya ce sai da fusatattun masu zanga-zangar suka lakada wa wanda ake zargin duka kafin su amince su mika shi ga ofishin ’yan sanda na Maroko.
Ya ce ba a kai ga gano wayar da aka sace ba saboda wanda ake zargin ya mika wa wani abokinsa da ya tsere da ita.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu, ya sake nanata cewa wannan lamarin ya nuna a fili cewa wasu bata-gari ne da suka fake da zanga-zangar #EndSARS don su yi sace-sace da kuma lalata dukiyoyin mutane.