✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gudanar gasar kamun kifi ta Argungu karo na 60

Bayan ziyarar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari garin Argungu ranar Alhamis 12 ga watan Maris 2020. A ranar Asabar da ta wuce ne sama da masunta…

Bayan ziyarar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari garin Argungu ranar Alhamis 12 ga watan Maris 2020.

A ranar Asabar da ta wuce ne sama da masunta dubu 30 suka shiga gasar kamun Kifi a kogin garin Argungu, wanda ake kira da suna Matan Fada.

Masunta cikin ruwa kowa na rububin kamun kifi a lokacin gasar

Shi dai wannan gasar kamun kifi an fara shi ne tun cikin shekara ta 1934 kimanin shekaru 80 ke nan, wanda aka gudanar a ranar Asabar 14 ga Maris 2020 shi ne gasar kamun kifi karo na 60.

Kafin ranar da za a gudanar da bukin kamun kifn tun daga ranar Laraba har zuwa ranar Asabar, an gudanar da wasannin gargajiya daban -daban wanda suka hada da: Wasan dambe da kokowa da sukuwar dawaki da kwallon dawaki da kuma gwajin kayayyaki na yakin Daular kanta, ana kuma tseran motoci, wanda a suke tasowa daga Abuja zuwa Argungu, akwai kuma wasan kabawa da kuma tseran kwalekwale da iyo da kuma kamun agwagwar ruwa da kuma nuna amfanin gona.

Dukkan wadannan wasanni an gabatar da su ne a cikin kwana biyu kafin ranar da za a gudanar da bukin kamun Kifi.

Jami’ai masu kula da gasar kamun kifi ke kokarin auna nauyin wani kifi da aka kama yayin gasar.     

A ranar Asabar 14 ga Maris 2020 da misalin karfe 10.30 na safe masunta sama da dubu 30 wadanda aka tantance suka tsundama cikin kogin Argungu domin kowa ya nuna gwanintarsa ta ganin kowa ya samu nasara ya zama zakara na wannan bukin kamun kifi na shekara 2020.

Masuntan sun samu kimanin awa daya da minti 20 a cikin kogin, an kama manya manyan kifaye sama da 100 amma daga cikin kifayen da aka kama, wanda ya samu babban kifi shi ne  Abubakar Ya’u daga karamar hukumar Augie jihar Kebbi. Wanda ya kama kifi mai nauyin kilogiram 78, mai bi masa wanda yazo na biyu shi ne Bala Yahaya Bagaye, wanda ya kama kifi mai nauyin kilogiram 75, shi ma ya fito ne daga karamar hukumar Augie  ta jihar Kebbi, wanda ya zo na uku shi ne Mai Wake Sani, daga karamar hukumar Silame jihar Sakkwato.

Gwarzon da ya zo na daya ya sami kyautar mota guda biyu da kudi sama da milyan 7 da kuma kujerun Makka guda biyu, shi kuma wanda ya zo na biyu ya sami kyautar mota da keken NAPEP da kudi sama da milyan hudu da kuma kujerar Hajji,  shi kuma wanda ya zo na uku ya samu kyautar babur da kudi sama da milyan uku da kujera Hajji guda daya.

Aminiya ta samu zantawa da wanda ya samu nasarar cin na daya inda ya ce, ya gode wa Allah subahanahu wata a ‘la da Ya sa ya shiga ruwan ga lafiya ya kuma fito lafiya, ya kuma kara da cewa koda bai kama komi ba, tunda ya fito lafiya to ya gode wa Allah, ballanta na ya samu nasara ya zo na daya daga cikin masunta sama da dubu 30, shi Allah ya zabe shi ya bashi sa’ar kamun kifin da ya fi na Kowa.

Ya kuma yi godiya ga Mai martaba Sarkin Kabin Argungu da Gwamnatin jihar Kebbi da suka shirya wannan bukin kamun kifi, domin inda ba su shirya wannan buki ba, da ban samu Wannan kyaututtuka ba wanda ban taba tsammanin zan same su ba har in bar duniya, na kuma kara godiya ga Ubangiji Allah.

Shi kuwa wanda yazo na uku, ya yi korafi ne inda ya ce yana ganin kifin da ya kamo kamar an mu sanya masa saboda shi ba dan jihar Kebbi bane, amma daga karshe ya ce kyaututtukan da ya samu Allah Ya sa masu albarka, kuma ya gode wa Allah da ya Sa ya fito lafiya.

Kasashen da suka halarci wannan bukin kamun kifi sun hada da: Nijar, Chadi, Kamaru, jihohin da suka shiga gasar kuwa su ne Kebbi, Zamfara, Sakkwato, Neja,  Yobe, Borno, Taraba, Kwara, Nasarawa, Filato, Bauchi, Kogi, Bayelsa, Gombe, da Adamawa.

Lokacin da Shugaba Buhari ya ziyarci Argungu