✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka gudanar da Hawan Daushe a masarautar Jama’a

Ya nuna haduwar musulmi da Kirista a wurin bikin a matsayin ci gaban da ya kamata a ririta shi.

Kamar kowace shekara, bikin Hawan Daushe na bana da aka gudanar a Masarautar Jama’a da ke Jihar Kaduna ya kayatar, inda Musulmi da Kiristoci suka hadu a Fadar Mai Martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II da ke garin Kafanchan tare da masu raye-rayen gargajiyarsu wajen gudanar da bikin.

Kamar yadda aka saba, a kowace shekara Sarkin da ayarinsa da ya kunshi mahaya dawaki da masu tafiya a motoci da babura da kekuna da kuma masu takawa a kafa kungiya-kungiya kan yi tattaki daga Kofar Fadar Sarkin zuwa Babban Asibitin garin domin gaishe da marasa lafiya tare da yi musu addu’a.

Lokacin da yake jawabi a asibitin, Sarki Muhammad Isa Muhammad ya bayyana godiyarsa ga Allah kan yadda aka gudanar da bukukuwan Sallah lafiya, inda ya yi kira ga al’umma su kasance masu biyayya da rungumar zaman lafiya.

Bayan addu’a ga marasa lafiyar, Sarkin yayi alkawarin ci gaba da taimakawa da abinda ya sawwaka tare da mika sauran bukatun da yafi karfinsa ga gwamnatin jiha.

Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad yayin ziyarar marasa lafiya a Babban Asibitin Kafanchan.

A jawabin Babban Daraktan Asibitin, Dokta Isaac Nathaniel, ya mika godiyarsa ga Sarkin bisa ga irin nuna damuwarsa ga marasa lafiya a lokacin da wadansu takwarorinsu da ’yan uwansu ke gidajensu suna bukukuwa da shagulgula.

Dokta Nathaniel, wanda Sakataren Asibitin ya wakilta, ya yaba wa Sarkin da kokarin ziyartar marasa lafiya a asibitin, inda ya mika godiyarsa ga gwamnatin Tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari bisa ga sauraron koke-koken da suke gabatarwa musamman a halin yanzu da take dasa na’urar shakar numfashi na Oksijin wanda irinsu guda tara ne kacal a Najeriya.

Wakilin Shugaban Karamar Hukumar Jama’a yayin da yake jawabi a Asibitin Kafanchan

“Da wannan muke mika godiyarmu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari duba da yadda gwamnatinsa ke kwazo da ba da gudunmuwar da za ta taimaka wajen ceto rayuka a maimakon sai an yi gaggawar kai su zuwa garuruwan Kaduna ko Jos ko Abuja,” in ji shi.

A cewarsa, akwai asibitoci da dama da ke Kudancin Kaduna da na makwabtan jihohi da za su amfana da na’urar da zarar an kammala hadawa.

Da yake bayyana kalubalen da suke fuskanta a asibitin, Dr. Nathaniel ya ce asibitin na fama da matsalar rashin isassun ma’aikata da rashin jami’an tsaron da za su rika kula da asibitin saboda a kan samu mabarnata su shiga su yi sace-sace.

Bayan kammala ziyarar ce Sarkin da jama’arsa da sauran baki suka dunguma zuwa Kofar Fadar don ci gaba da bukukuwa, inda tawagar masu rawunna da suka hada da Lifidin Jama’a da Danmadamin Jama’a da Sarkin Gandun Jama’a da Ajiyan Jama’a da Gado da Masun Jama’a da Wakilin Tsafta da kungiyar maharba da ta matasa suka yi sahu-sahu wajen gaishe da Sarki da ke tsaye bisa dokinsa yana karbar gaisuwar masu rawanin.

Sarkin Jama’a da Sakataren Karamar Hukumar Jama’a, Isa Musa a fadarsa bayan dawowa daga Hawan Daushe

Da yake jawabi, Babban mai Masaukin Baki kuma Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Kwamared Yunana Markus Barde, ya taya Sarkin da sauran al’ummar Musulmi murnar yin bukukuwan Sallah lafiya, inda ya kara jaddada kiransa na bunkasa harkar zaman lafiya a yankin wanda a sanadiyyar zaman lafiyan ne har ake iya gudanar da bukukuwa da shagulgula cikin kwanciyar hankali.

Da yake nasa jawabin, Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Mazabar Jama’a, Ali Kalat, ya bayyana farin cikinsa kan halartar bikin karo na farko a rayuwarsa, inda ya nuna haduwar musulmi da Kirista a wurin bikin a matsayin ci gaban da ya kamata a ririta shi.

Bayan taya masarautar Jama’a da sauran al’ummar musulmi murnar gabatar da sallah lafiya, ya kuma yi alkawarin daukaka korafe-korafen da shugaban asibitin ya yi da sauran bukatu na asibitin zuwa ga gwamnatin Jihar Kaduna da sauran masu ruwa da tsaki don magance matsalolin asibitin tare da kaddamar da ayyukan jin kai kyauta ga marasa lafiya masu karamin karfi.

Aminiya ta ruwaito cewa, bikin sallar na bana ya samu halartar kungiyoyin makada da mawaka da suka hada da ’yan kabilar Koro da ’yan rawar kwarya daga Karamar Hukumar Kagarko da makadan kabilar Jarawa da na Fantswam da masu busar algaita da kungiyar maharba, wadanda suka nishadantar da mahalarta taron.