✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gudanar da bikin Tande a Nijar

A kwanakin baya ne aka gudanar da bikin Tande a Jihar Agades da ke kasar Nijar. An gudanar da bikin ne a gidan wasa na…

A kwanakin baya ne aka gudanar da bikin Tande a Jihar Agades da ke kasar Nijar.

An gudanar da bikin ne a gidan wasa na Samariy Sabon Gari Unguwar Zabarkan da ke birnin Yamai karkashin kulawar kungiyar Taghlamt.
Biki ne da ake gudanarwa duk ranar 15 ga Zulhijja na kowace shekara don nuna farin cikin an yi sallar layya lafiya.
Shugaban kungiyar Taghlamt kuma Kodinetan shirya bikin na bana ya ce “Tande suna ne na wani nau’in kayan kida da rawa na al’adar Buzayen kasar Nijar. Ya kasu kashi biyu. Na farko wasan da ake yi a kan rakuma ta hanyar sarrafa rakumi ya yi duk abin da ake so. Akwai sukuwa da kuma rawa da rakumi ta hanyar bin kidan da ake yi masa.”
Ya ce na biyu kuma wasan da samari da ’yan mata ke yi da daddare. A tsakiyar babbar da’irar masu rawa za su shigo su zauna a gaban makada. Layin maza yana kallon na mata. Ita rawar zaune ce ana rausaya ana tafa hannuwa da girgiza kai tare da yin kuwwa. Rawa ta biyu ita ce rawar da ake yi ta tsaye tare da diddira kafafu.
daya daga cikin matan da suka halarci bikin Salamatou Mamman ta bayyana irin tufafin da mata suke sanyawa yayin bikin.
Ta ce: “Ana yin shiga ta al’ada, inda mata ke sa bakaken kayan na alfarma da ake kira ‘Turkudi’, sannan a hadu a rukuni-rukuni. Za a dafa abinci.”
Ta ce akwai muhimman abubuwa uku da ke faruwa a wajen wannan wasa. Na farko a nan ne ake zabar budurwar da tafi kowa kyau a wannan shekara. Sai zabar macen da tafi kowa iya abinci, daga nan ne saurayi zai fitar da wadda zai aura ta hanyar yi mata wata kyauta a gaban jama’a.
Mamman Issa daya daga cikin manyan baki a wurin bikin ya yi bayanin ire-iren bukukuwan da ake yi a kasar Nijar.
Ya ce: “Akwai wani wasan da ake kira, ‘Biyano’. A garin Ingal ta Agades ake yinsa. Ana fita wajen gari a kwana, washegari a yi jerin gwano tare da masu tarba zuwa fadar sarki. A Jihar Diffa wasan ‘Sumaro’ ake gudanarwa; wasa ne na algaita, yadda ake busarta da raye-rayenta da sauransu. Ita kuwa Jihar Damagaran wasan ‘Sallar Gayi’ ake yi. Shi ma ana fita wajen gari ne a kwana, amma yanzu an bar yi saboda muninsa. Ita kuwa Jihar Maradi wasa ne na Fulanin Dakwaro.”
Bikin na bana ya samu halartar jama’a masu yawa, an kuma kammala taron lafiya.