Shugaban Kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ya bayyana yadda diloli suka riƙa yi wa kamfanin ƙafar-ungulu a shirinsa na sayar da kowane buhun siminti a kan farashin N3,500 a bara.
Da yake jawabi a wurin taron shekara-shekara na kamfaninsa a Abuja ranar Alhamis, Abdulsamad Rabiu ya ce zalamar da diloli suka riƙa yi ta neman ƙazamar riba ce ta sa suka riƙa ƙara kuɗi a kan farashin simintin.
- An sauya ranar zaɓen ƙananan hukumomin Kano
- NNPCL zai mayar da ɗawainiyar matatun mai hannun ’yan kasuwa
A cewarsa, “Diloli da dama sun yi amfani da damar da muka bayar ta karya farashin siminti don cimma manufarsu mara kyau. Maimakon su ƙara riba kaɗan a kan farashin da muka sayar musu, sai suka riƙa ninka farashinsa.
“Wasu daga cikinsu sun riƙa sayar da kowane buhu ɗaya na siminti a kan N7,000 zuwa N8,000. Ba ƙaramin kuɗi suka samu ba.
“Ina tsammani mun sayar da fiye da tan miliyan ɗaya a kan N3,500 kafin mu fahimci abin da dilolin suke yi,” in ji shugaban Kamfanin BUA.
Ya ce, “Mun so farashin ya tsaya a yadda yake amma diloli suka ƙi. Don haka, babu yadda za mu iya ci gaba da sayar da shi a kan wancan farashin domin kuwa tamkar diloli kaɗai muke bai wa tallafi.”
Abdulsamad Rabiu ya ƙara da cewa karyewar farashin Naira da cire tallafin man fetur su ma sun taimaka wajen rashin ɗorewar shirin nasa na karya farashin siminti.
“Ina nufin lokacin da farashin dalar Amurka ya tashi daga kusan N600 zuwa kimanin N1,800. Saboda haka wannan lamari ya kasance babban ƙalubale a gare mu wajen rashin ɗorewar shirin na karya farashin siminti.”