✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka cafke dan bindiga yayin kai hari a Kaduna

Dubun wani dan bindiga ta cika bayan musayar wuta a kauyen Madugu da ke babbar hanyar Galadimawa zuwa Tumburtu da ke Karamar Hukumar Giwa ta…

Dubun wani dan bindiga ta cika bayan musayar wuta a kauyen Madugu da ke babbar hanyar Galadimawa zuwa Tumburtu da ke Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

’Yan sanda sun cafke dan bindigar ne a ranar Alhamis, sannan suka kwace babura biyar na abokan ta’addancinsa da suka tsere bayan sun sha luguden wuta.

Kakakin ’yan sanda ta Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ce bayan samun rahotanni kan ayyukan bata-garin a hanyar ne aka tura jami’ai daga rundunar Operation Whirl Punch suka fatattake su.

Ya ce bayan musayar wutar, ’yan bindigar sun tsere bayan yawancinsu sun samu raunukan harbi, suka bar baburansu guda biyar, amma an kama mutum daya daga cikinsu.

Ya ce a lokacin da suke masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi dan bindiga ne, kuma an kai kayan da aka kwace a hannunsu zuwa ofishin ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

Jalige ya kuma shawarci mutanen yankin da su kai wa jami’an tsaro rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi.