✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Aka Biya N50,000 don Kallon Wasan Kwaikwayon Sarki Sunusi A Legas

Sarki Sanusi II halarci taron wasan kwaikwayo kan sauke shi daga karagar mulki

An gabarta da wani wasan kwaikwayo na dabe kan tarihin rayuwar Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sunusi II da kuma kakansa Sarki Muhammadu Sunusi I a Legas.

An yi  wasan ne a wani dakin taron na alfarma a daren Asabar, ya kuma burge ’yan kallo ciki har da dalibai.

Wasan wanda aka yi shi da harshen Ingilishi da taken “Gaskiya A Cikin Zamunna”, waiwaye ne kan tarihin Sarkunan Kano biyu.

Sarakunan biyu sun sauka daga mulki ne bisa wasu dalilai da ta kai ga gwamnatocin zamunansu sun sauke su daga kan karagar mulki.

A cikin wasan, an nuna yadda hakan ta faru ne ta hanyar labarin gidan wani tsohon dogari da dansa wanda ya gaje shi a fada, da kuma matarsa

Tsohon dogarin ya yi zamani da Sarki Sunusi I har ya sauka, sai ga shi kuma da ransa a zamanin dansa wanda ya gaje shi a fada, Sarki Muhammadu Sunusi II ya bar karagar mulki.

Wanda aka yi wasan a kansa, Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sunusi II, ya halarci nunin wasan tare da wasu manyan mutane daga ciki da wajen Legas, da kuma dalibai daga wasu makarantun jihar.

Mafi karancin kudin shiga kallon wasan shi ne Naira 5,000, na masu alfarma kuwa shi ne N20,000 da kuma na kasaittatu N50,000.

Kamfanin da ya shirya wasan ya ce zai yi irinsa kan tarihin wasu ’yan Najeriya, kamar su shahararriyar mai gina tukwane, Ladi Kwalli ta Abuja.

A baya, kamfamin ya yi irin wannan wasa kan marigayi Cif Obafemi Awolowo da kuma Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.