✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyo: Yadda Abudulmumin ke durkusawa shugaban APC na Kano

Alamu sun nuna cewa, Abdulmumin Jubril Kofa ya himmatu don ganin ya dinke barakar da ke tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kano gabanin…

Alamu sun nuna cewa, Abdulmumin Jubril Kofa ya himmatu don ganin ya dinke barakar da ke tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kano gabanin zaben cike gurbin da za a yi a mazabarsa.

Dan majalisar wanda dangantakarsa tayi tsami tsakaninsa da Gwamnan jihar Kano da sauran shugabannin jam’iyyar APC a jihar, inda wani faifan bidiyo ya nuna ya duka yana mika gaisuwa ga shugaban jam’iyyar Alhaji Abdullahi Abbas, a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Bidiyon da aka yada a kafafan sadarwa na sada zumunta ya dauki hankalin jama’a da dama musamman magoya bayan jam’iyyar ta APC wadanda ke sane da irin danbarwar da ke tsakanin Dan majalisar da shugabannin jam’iyyar a Kano, sun kadu da ganin faifan bidiyon duba sakamakon abin da ya faru a baya.

A baya an zargi Dan majalisar da yi wa jam’iyyar adawa aiki a lokacin zaben watan uku na shekarar da ta gabata, tare da kin yin biyayya ga jam’iyyarsa lamarin da ya sanya jam’iyyar ta dakatar da shi na tsawon watanni 12 bayan kwamitin da ya yi aikin bincike akansa ya gabatar da rahoton bicikarsa.

Shugaban jam’iyar APC Alhaji Sabo Gwarmai, wanda a lokacin ya tabbatar da dakatar da Kofa, ya bayyana cewa laifukan da dan majalisar ya aikata sun yi kamari ta yadda ba za a iya kau da kai ba sannan dole ne a hukunta shi.

Binciken da Aminiya tayi ta gano cewa, tun bayan da Dan majalisan ya lashe zabensa ya yi watsi da al’amuran jam’iyyar APC, har sai da kotun daukaka kara a Kaduna ta soke zabensa inda ta bada umarnin sake yin zabe a mazabarsa, tun daga wannan lokacin ne dan majalisar ya fara kamun kafa daga jigajigan jam’iyyar da suka hadar da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Gaya da kuma shugaban jam’iyyar Alhaji Abdullahi Abbas, a kokarin da yake na sake komawa majalisar.

Kafin bayannar faifan bidiyon an ga hoton dan majalisar a durkushe yana gaisawa da Sanata Kabiru Gaya, a wani gida da ake zaton a Abuja ne, sannan bayan da kotun daukaka karar zabe ta soke zabensa an ganshi a gidan Gwamnatin Kano yaje taya gwamna Ganduje murna.

Tsohon dan majalisar tare da wasu fitattun ‘yan siyasa sun je tashar tashi da saukar jiragen sama ne domin tarbar shugaban majalisar kwana biyu bayan da kotun koli ta tabbatarwa gwamna Ganduje kujerarsa ta gwamnan jihar.

A baya bayanai sun nuna cewa, jam’iyyar APC ba zata goyawa dan majalisar baya ba a zaɓen cike gurbin duba da kamarin dangantakarta da dan majalisar, sai dai shugaban jam’iyyar Alhaji Abdullahi Abbas, ya ce jam’iyyar zata tabbatar mazabar Tudun Wada/Doguwar da Kiru/Babeji bata kubuce mata ba.

Shugaban jami’iyyar ya bayyana cewa, Gwamna Ganduje da sauran jigajigan jam’iyyar zasu je kamfe a mazabun Doguwa da Tudun Wada domin nema wa Alhassan Ado Doguwa goyon bayan jama’a sai dai ba a kai ga yanke shawarar zuwa mazabun Kiru da Bebeji ba wato mazabun dan majalisa Kofa ba.

Ya ce, “A yau Alhamis wakilan jam’iyyar zasu kasance a Doguwa da Tuduna Wada suyi wa Alhassan Doguwa kamfe, Gwamna Ganduje da sauran manyan ‘yan jam’iyyar zasu kasance a wajen kamfe.”

“Shirye shirye sun kammala kana ina baku tabbacin cewa, APC zata yi wa Doguwa kamfe kamar yadda ya dace, “Amma bamu kai ga yanke lokacin da zamu je Kiru da Bebeji ba, amma ina baku tabbacin zamu yi duk abin da ya dace mu tabbatar mun sami nasara.” in ji shi.

Da yake tsokaci akan bidiyon shugaban jam’iyyar ya shaida cewa, abun da ya faru a bidiyon ba bakon abu bane, “Wannan ya zamo kuma labari? Honorabul Abdulmumin Jubril Kofa, ya tarbe mu a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, ba Kofa kadai ya tare mu ba, ni banga abin damuwa a tarar da Kofa ya yi mana ba.” In ji shi.