Sanatan Kano ta Tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira da a guje wa yada labaran karya da cewa hakan na zubar da kimar kowane mutum mai aikata hakan.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano ya fadi hakan ne a wurin wani taron bita ga ’yan Soshiyal Midiya da aka gudanar a gidansa domin fahimtar da su game da yadda za su rika tallata manufarsa da kuma yadda za su guje wa yada labaran karya.
Sanata Ibrahim Shekarau ya bukaci mahalarta taron su guji yada labaran karya koda kuwa a kan ’yan hamayya ne, domin a cewarsa yin karya yana zubar da kimar dan Adam.
“Ku guji yin kalaman batanci a kan kowa saboda abin da ka yi kai ma shi za a yi maka.
“Idan ka bata gwanin wani, shi wanda ka bata wa gwaninsa shi ma zai bata naka gwanin. Ka ga an-yi- ba- a- yiba ke nan,” inji shi.
Sanatan ya ce bai shirya taron da wata manufa ba illa don wayar da kan ’yan soshiyal midiyar nasa kan yadda za su guje wa yada kalaman batanci.
A cewarsa, kusan shekara guda ke nan yana ta son shirya irin wannan bita saboda a daina yada labaran karya da na batanci domin daidaita al’amura.
“Na san wadansu za su yi tunanin an shirya wannan taron saboda abin da ke faruwa a cikin jam’iyyarmu.
“To, ina mai sanar wa kowa cewa wannan taron ba ya da alaka da wannan matsalar.
“Wannan daban wancan ma daban. Kuma idan lokacin wancan ya yi za mu yi magana a kai,” inji shi.
Masana da dama ne suka fadakar da mahalarta taron cikinsu har da Daraktan Watsa Labarai na Sanata Shekarau, Dokta Sule Ya’u Sule.
Mahalarta taron sun bayyana jin dadinsu game da wannan bitar da Sanatan ya shirya musu inda suka yi alkawarin yin aiki da abin da suka koya.