✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi masa yankan rago a kan bazawara

Ana zargin wani matashi mai suna Ya’u Haruna wanda ya fito daga Qaramar Hukumar Sule Tankarkar da ke Jihar Jigawa da laifin yi wa wani…

Ana zargin wani matashi mai suna Ya’u Haruna wanda ya fito daga Qaramar Hukumar Sule Tankarkar da ke Jihar Jigawa da laifin yi wa wani mutum yankan rago a kan bazawara.

Matashin mai kimanin shekara 25 ana zarginsa ne da yi wa abokin takararsa yankan rago a dajin Barde.
Majiyarmu ta ce matashin da ake zargin ya shaida wa ’yan sanda cewa sun jima suna musayar saqo ga juna amma ba su samu haxuwa ba sai a wannan karon da suka haxu a dajin ne sai marigayin mai suna Haruna Dakuku ya fara takalarsa da faxa a dajin shi ne suka kama kokawa sai ya qwace sandar da ke hannun marigayin ya buge shi.
Majiyar ta ce ya faxa wa ’yan sandan cewa faxuwar marigayin ke da wuya sai ya zaro wuqa ya yi masa yankan rago kuma ya yi gaba da dabbobin da marigayin yake kiwo zuwa gidansu.
Majiyar ta ce sakamakon bincike ne aka kama shi aka miqa wa ’yan sanda waxanda suka gurfanar da shi a gaban kotu.
Lokacin da aka gabatar da wanda ake tuhumar a gaban Kotun Majisatre ta Dutse ya amsa laifinsa sai dai ya yi nadamar faruwarar lamarin.
Mai gabatar da qara ya shaida wa alqalin kotun, Mai shari’a Usman Muhammed Lamin cewa laifin da ake tuhumar matashin ya sava wa sashi na 220 da 296 na dokokin FInal Kod. Alqalin kotun ya bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhumar sai ranar 28 ga Maris domin bai wa ’yan sanda ci gaba da bincike, yayin da kotun za ta samu cikkaken lokaci don yin nazari a kan shari’ar