Wani mara lafiya, Adelano Salawu, ya fada cikin rafi da nufin kashe kansa saboda ya kasa biyan kudin magani a Osogbo, babban jihar Osun.
Da taimakon mutanen unguwar Gbodofon, inda rafin ya ke, aka ceto rayuwar Salawu mai shekara 50 a duniya.
A jawabinsa, bayan an ceto shi daga cikin rafin, Salawu ya ce ya kwanta asibitin kudi na tsawon makonni kafin likitoci su ce masa ciwonsa na bukatar a mayar da shi asibiti kwararru na Jami’ar Ladoke Akintola.
Ya ce “bai je asibitin jami’ar ba saboda ba shi da kudin da zai biya a kula da lafiyarsa.”
“A hanyar koma wa gida ne na suma, sai motar daukar marasa lafiya ta dauke ni ta kai ni asibitin jam’iar.”
“A asibitin an bukaci na biya Naira dubu 150 kafin su yi min magani, amma daga bisani suka sallame ni saboda sun fihimci ba ni da su.”
“Da radadin ciwo ya kama ni kuma na ga ba ni da wata hanyar samun kudi ya sanya na yanke shawarar na kashe kaina.”
Ya roki gwamnatin jiha da masu hannu da shuni da su taimaka su biya kudin don ya samu lafiya.