✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi gudun kilomita 600 zuwa gida a kasar Sin

Wani mutumin kasar Sin, mai suna Huang changyong, dan shekara 33, ya ruga zuwa gida, inda ya share kilomita 600 don halarta wasannin sabuwar shekara.…

Wani mutumin kasar Sin, mai suna Huang changyong, dan shekara 33, ya ruga zuwa gida, inda ya share kilomita 600 don halarta wasannin sabuwar shekara. A irin wannan lokaci, mafi yawan al’ummar kasar sin da ke zaune a wasu sassan kasa, na garzayawa zuwa garuruwansu na haihuwa, inda sukan yi rububin hawan motocin bas-bas da kananan motocin hawa da Babura. Shi kuwa wannan matashi sai ya aikata sabanin yadda mutane suka saba yin tafiya mai nisa a wannan zamanin.
Huang dai tuni ya tsara yadda zai shafe kwana tara yana gudu har zuwa gidan su, da ke birnin Shenzhen, a kudancin kasar Sin da ke Lardin Guangdong a garin Chengzhou da ke tsakiyar kasar Sin a gundumar Hunan.
A tsarin gudun wannan matashi, ya shirya yadda zai rika share kilomita 70 a kowace rana, har ya cimma adadin tafiyarsa zuwa na tsawon kilo0mita 600.
Wannan matashi ya isa garin su a yau Juma, 29 ga watan Janairun bana. Dama shi dan wasan gudu, wanda ya shafe shekara 18 yana tsere. Kuma a lokacin da yake yin wannan gudun, mutane da dama sai tsayar da shi suke yi don su dauki hoto tare da shi. Ya ce, ya kara samun kwarin gwiwa a wannan tseren da ya yi zuwa gida, a daidai lokacin da ya gane cewa yana ta kusantowa zuwa gida.