✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya rasu saboda an zura kwallo a ragar Arsenal

Wani mai goyon bayan kulob din Arsenal da ke zaune a Jihar Imo mai suna Dominic Ejimba rahotannin sun nuna a ranar Asabar da ta…

Wani mai goyon bayan kulob din Arsenal da ke zaune a Jihar Imo mai suna Dominic Ejimba rahotannin sun nuna a ranar Asabar da ta wuce ne ya rasu sakamakon kwallon da kulob din Stoke City ya zura a ragar Arsenal a gasar rukunin firimiya ta Ingila mako na biyu.

Stoke City ce ta samu nasara a wasan da ci 1 mai ban haushi.

Rahotanni sun nuna al’amarin ya faru ne a karamar Hukumar Isiala Mbalo ta Jihar Imo a lokacin da Dominic Ejimba ya halarci wani gidan kallon kwallo don ganin yadda wasan zai kaya a matsayinsa na daya daga cikin ’yan-ga-ni-kashenin kulob din Arsenal.

Kamar yadda wadanda al’amarin ya faru a kan idonsu suka nuna, sun ce an ga matashin ya yanke jiki ya fadi ne jim kadan bayan an zura kwallo a ragar Arsenal, inda wasu suka yi hasashen watakila ya shiga wannan hali ne saboda cacar kwallo.  Duk kokarin da aka yi don a ceto shi al’amarin ya ci tura kuma kafin a kai shi asibiti ne rai ya yi halinsa.

Kafofin watsa labarai sun tabbatar wani kanin mamacin mai suna Francis Onwuka ya tabbatar da wannan labari, inda ya nuna dan uwansa ya rasu ne sakamakon kwallon da aka zura a ragar kulob din Arsenal.

Dominic Ejimba yana daga cikin ’yan-ga-ni-kashenin Arsenal, don haka da yawa ba su yi mamakin abin da ya faru da shi ba.

Al’amarin mutuwar masu goya wa wani kulob baya a sassan duniya ba sabon abu ba ne musamman a Nahiyar Afirka, don an shawo kawo rahotannin da ke nuna yadda magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa daban-daban suke mutuwa saboda takaicin yadda ake doke kulob din su.