✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya rasa barin kansa sakamakon shan lemon kara kuzari

Ba zan rabu da shi ba, saboda ina kaunarsa fiye da ita rayuwar kanta.

Wani mutum mai suna Austin a Jihar Kalifoniya ta kasar Amurka ya rasa wani bari na kokon kansa sakamakon yawan shan lemon kara kuzari.

Wata mata mai suna Brianna ta wallafa labarin mutumin a shafin Endres Photography a Facebook, inda ta bayyana yadda yawan shan lemukan kwalba masu kara kuzari ya sa mijinta ya rasa wani bari na kokon kansa.

Brianna ta ce, mijin nata Austin ya fara samun matsala ce sakamakon shan lemukan kara kuzari da yake yi a lokacin aiki.

“Abin ya samo asali ne lokacin da yake bata awanni wajen yin aiki da dare, ga shi abin na neman zama barazana ga rayuwarsa.

“Wani lokaci ina barci, surukata ta tashe ni cewa an kai mijina asibiti ba lafiya,”inji ta.

Ta ce, daga baya an yi mata bayanin cewa ya samu ciwo a kwakwalwarsa kuma ya yi doguwar suma.

A bincike da gwaje-gwajen da likitoci suka yi sun gano cewa yawan shan lemon kara kuzari ne ya haifar masa da ciwo a kwakwalwa.

Austin da Brianna

Likitoci sun yi wa Austin aiki daban-daban a kwakwalwarsa, inda a wasu lokatu ya sha fama da ciwo iri-iri.

Kuma a sanadin haka ne ya sa likitoci suka zaftare wani bangare na kansa don nema masa sauki.

Yanzu haka Brianna tana dauke da cikin wata tara na Austin.

Matar ta ce, yanayin da take ciki ba mai sauki ba ne sakamakon fama da juna biyu da kuma hidimar kula da mijinta.

“Ina dafa masa abinci, in koya masa tafiya da magana, sannan in kula da shi sosai. Ina taimakon sa ta duk wani bangare na rayuwarsa,” inji Brianna.

Ta ce, duk da irin fadi-tashin da suke fama, ba za ta rabu da mijinta ba saboda soyayyar da take masa ba ta wasa ba ce.

“Ba zan rabu da shi ba, saboda ina kaunarsa fiye da ita rayuwar kanta,” inji Brianna.