A matsayinki na ’ya mace wacce ta fara mallakar hankalin kanta, mahaifiyarki ce ta fi kusanci da ke. Kuma ita ce wacce ya kamata ki rika shawarta a dukkanin lamuranki maimakon kawaye ko saurayi. duk da cewa babu laifi wajen neman shawarar kawayen da kuma saurayi to amma abin da ya sa a kullum nake kalubalantar wannan dabi’a ta maida kawa ko saurayi abokin shawara ba komai ba ne illa irin yadda wasu ’yan matan kan jinginar da mahaifiya a lamuransu, wanda hakan ina ga kuskure ne babba ba karami ba. A matsayinki na uwa wani abin kece kawai za ki dau haske ki shiga lamuran ’yar ki ko da ba ta sanar dake ba.
Wasu iyayen sun dauka kawai su yarinya ta ci ta sha, a kora ta islamiyya ya wadatar ba ta bukatar wani dan taro ko sisi domin biyan wasu bukatun ta na musamman. Dan’uwana kanwarka ko yayarka in ka ji da dan canji a aljihunka daure ka ba ta wani abu, wa ta ma za kaga tambayarka za ta yi to dan Allah a rika daurewa ana basu lokaci zuwa lokaci ko dan gudun kada ta rika tambayar saurayinta. Dan kayan kwalliyar nan a rika daurewa ana siyawa kanne. Wallahi wata kayan kwalliyar ma ta dogara ga saurayi ne, idan kanwarka ta zama haka komai na iya faruwa. Ka riga ka san halinmu samarin zamani.
Abin zai baka mamaki ka ji yarinya na tambayar saurayin ta wani dan adadin kudi wanda bai taka kara ya karya ba. Illar dake tattare da tambayar saurayi kudi Allah kadai Ya san iyakarta, domin ta na daga cikin hanyoyin dake haifar da alakar banza a tsakanin masoya. Ba yadda za a yi wani saurayin ya dau kudi ya baki ba tare da ya taba jikin ki ba, idan ma bai fara taba ki a farko ba, idan tafiya ta yi nisa ya na iya zuwa miki da wannan mummunar bukatar. Yana da kyau idan ki na da wata yar bukata ta kudi ki tambayi mahaifiyarki ko mahaifinki ko yayanki maimakon saurayi.
Abin zai baka mamaki matuka yadda ’yan mata da yawa ba sa rufe sirrinsu ga samarinsu, duk halin da suke ciki ko yanayin da suke suna iya sanarwa da samarinsu. Idan kika yi abu da saurayinki kwata-kwata ki daina tunanin sirri kuka yi. Wani da zarar ya bar wajen ki ko
makwancinsa ba zai nufa ba, har sai ya nemi wani ko wasu daga cikin abokanansa ya sanar musu. Duk saurayin da zai taba jikinki ko kuma ya nemi yin lalata dake wai kuma ya bude baki yace miki wai saboda tsabar son da yake miki ne yasa to karya yake, da zarar ya biya bukatarsa ba shashasha irinki a wajensa, kuma yana iya rabuwa dake a kowane lokaci.
Kamar yadda ba zaka so wani ya lalata kanwarka da sunan yana son ta ba, to kai ma kada ka lalata kanwar wani wai da sunan ka na sonta karya kake.
Ki tsoraci saurayi mai hirar banza idan kuna a tare ko kuma in kuna waya da shi. Idan kina son shi da gasken-gaske yi kokari ki ga ya daina, idan kuma bai daina ba ki yi maza ki hanzarta cire shi a zuciyarki tun kafin ya fara aikata irin abubuwan da bakinsa ke fada.
Wani sa’in ’yan mata ina ga laifinku domin kuwa duk lalacewar mutum ina ga sai kin amince zai taba jikinki in kuma ya ki kiyi masa barazanar rabuwa da shi. Idan saurayinki munanan halayensa suka bayyana kada ki biye masa. Duk yadda za a yi danne zuciyarki kada ki boye masa, in ta kama da rabuwar ma ku rabu insha Allahu, Allah Zai kawo miki wanda ya fishi. In kuma kina ga cewa ba za ki iya rabuwa da shi ba kika biye masa to karshenki dai nadama domin shi abu ne mai sauki ya guje miki da zarar bukatar sa ta biya.
Nasiru Kainuwa Hadeja
08100229688