Shafukan sada zumunta a kasar China sun yada wani rahoto da ya jawo muhawara kan wani labari mai cike da ce-ce-ku-ce na mutumin da ya kai karar agolansa bayan ya saki mahaifiyarsa, inda ya nemi a biya shi diyyar rainonsa.
Bayan ’yan watanni da rabuwa da matarsa, an bayar da rahoton cewa, mutumin mai suna Tang, wanda ya fito daga garin Chongking, ya kai agolansa mai suna Liu kotu, inda ya nemi a biya shi Yuan 35,200 (kimanin Dala 5,285, daidai da Naira miliyan 2 da dubu 195 da 230 da kwabo 45) a matsayin diyyar kudin da ya kashe wajen rainonsa.
- Jami’an tsaro sun yi bakin kokarinsu wajen kare gidan yarin Kuje —Dingyadi
- Yadda uwargida za ta adana naman Layya
An bayar da rahoton cewa, Tang ya auri mahaifiyar Liu a shekarar 2009, lokacin Liu yana da shekara 10 kuma ya taimaka wajen rainonsa har zuwa shekarar 2021, lokacin da matar ta shigar da kara kotu tana neman su rabu.
Kimanin wata uku bayan rabuwar ce, Tang ya shigar da kara a gaban kotu kan agolan nasa, inda ya nemi ya biya shi Yuan 30,000 daidai da Naira miliyan 1 da dubu 855 da 241 da kwabo 34 a matsayin kudin gudanar da rayuwar Liu.
Mummunar takaddamar shari’a ta musamman ta haifar da fushi a tsakanin miliyoyin jama’ar da suka kalli faifan bidiyon da aka wallafa a shafin Intanet na China, mai suna ‘Sina Weibo’.
Yawancin wadanda suka yi tsokaci sun zargi Tang da daukar fansa a kan agolansa bayan aurensa ya mutu da mahaifiyar yaron.
“Tang ya fara taimaka wa Liu ne bayan ya auri mahaifiyar Liu. Yanzu Tang yana son a dawo masa da kudinsa, wannan ya zama kamar wani abu ne mai kyau bayan auren ya mutu,” kamar yadda wani mutum ya rubuta.
“Kodayake ya raini yaron na tsawon shekara 10, da alama bai taba daukarsa da ba. Wannan abin bakin ciki ne,” inji wani da ya yi sharhi.
Wasu sun yi mamakin ko Tang ba ya tunanin tsohuwar matarsa za ta iya neman diyya saboda wahalar da ta sha a lokacin aurensu.
An yi sa’a wata kotun garin Chongking ta ki amincewa da bukatar Tang, inda ta yanke hukuncin cewa ai ya biya kudaden da yake neman diyya ne bisa radin kansa.
“Tang ya zabi ya tallafa wa Liu, duk da sanin cewa ba ya da hakki a shari’a na biyan kudin karatun jami’arsa saboda Liu ya kai shekara 18, a tsarin dokar kasa,” inji alkalin kotun.
A kasar China, yara kan kasance manya ne a bisa doka idan sun kai shekara 18, kuma ba a sa ran iyaye su biya bukatun rayuwarsu a wannan lokaci.