✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya mutu bayan dirowa daga bene mai hawa 7 a kokarin tserewa jami’an EFCC

Rahotanni sun ce mutumin da EFCC ke kokarin kamawar ba shi da kowacce irin alaka da wanda ya mutun

Wani mutum da ba a kai ga tantance wanene ba ya mutu bayan dirowa daga hawa na bakwai na wani bene dake rukunin gidajen 1004 a unguwar Victoria Island a Legas.

Mutumin dai ya diro daga benen ne ranar Alhamis a kokarinsa na tserewa jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC da suka je domin kama wani wanda suke zargi.

Rahotanni sun ce mutumin da EFCC ke kokarin kamawar ba shi da kowacce irin alaka da wanda ya fado daga benen kuma ya mutu.

Tuni dai aka mika batun nasa zuwa sashen binciken laifukan da suka shafi kashe kai na Sashen Binciken Manyan Laifukan ’Yan Sandan Jihar domin fadada bincike.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda jihar, Muyiwa Adejobi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce mutumin, wanda ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance shi ba ya mutu ne bayan fadowa daga hawa na bakwai na wani bene a unguwar Victoria Island a Legas.