✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mutu a lokacin da yake kwallo

Wani dan kwallon kulob din Mlbao da ke Tanzaniya mai suna Ismail Mrisho Khalifan ya yanke jiki ya fadi a lokacin da kulob dinsa yake…

Wani dan kwallon kulob din Mlbao da ke Tanzaniya mai suna Ismail Mrisho Khalifan ya yanke jiki ya fadi a lokacin da kulob dinsa yake karawa da na Mwadhi FC a ranar Lahadin da ta gabata a gasar cin kofin kwallon kafa na ’yan kasa da shekara 20 da Hukumar kwallon kafa ta Tanzaniya ta shirya.

Kamar yadda bayanai suka nuna, Marigayi Khalifan dan kimanin shekara 19 ya yi taho-mu-gama- ne da dan kwallon bayan kulob din Muwadhi minti 16 kafin a kammala wasan inda nan take ya fadi sumamme. Duk kokarin da aka yi don ya farfado abin ya ci tura al’amarin da ta sa aka garzaya da shi wani asibiti mafi kusa inda a can ne ya ce ga-garinku.
“Mun samu labarin rasuwar dan kwallon kulob din Mlbao kuma mun aika da sakon ta’aziyya ga iyalansa da abokansa da kuma daukacin al’ummar Tanzaniya”, a wata takarda da Hukumar shirya kwallon kafa ta Tanzaniya ta fitar.
Mutuwar Ismail Mrisho Khalifan dai ta zo ne kasa da wata daya bayan wata ’yar kwallon Gambiya Fatim Jawara ta gamu da ajalinta a kokarin haurawa kasar Turai. Ta rasu ne a wani gari da ke Libya bayan kwale-kwalen da take ciki ya samu matsala kuma ta kwashe kwana da kwanaki a daji ba tare da abinci ba.