✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mari matarsa ta mutu kan Naira 100

Wani magidanci mai suna Onyekachi Anele ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa mai suna Chikodi a sakamakon falla mata mari da ya yi, bayan takaddama ta…

Wani magidanci mai suna Onyekachi Anele ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa mai suna Chikodi a sakamakon falla mata mari da ya yi, bayan takaddama ta sarke a tsakaninsu kan Naira dari daya.
Wannna lamari ya faru ne a kauyen Obiniezena na karamar Hukumar Owerri Jihar Imo. Bayanan da Aminiya ta samu game da rikicin wanda ya yi sanadiyyar ajalin matar shi ne Naira 100 ce ta jawo wa ma’auratan cacar baki. Matar ce ta tambayi mijin da ya ba ta kudin da take binsa bashi, Naira 100. Shi kuma ya kekasa kasa ya ki ya ba ta, lamarin da har ya kai su ga musayar kazaman kalamai tsakanin juna. Sanadin haka shi kuma ya fusata ya wanke ta da  mari, ita kuma da ta ji zafi ta mayar masa da martini, shi ma kuma ya sake marinta. Marin nata ke da wuya ta zube kasa a some, daga nan ba ta farfado ba har sai da aka garzaya da ita asibiti, kafin a karasa asibiti ne ma ta ce ga garinku nan.
Yanzu haka Anele, mijin matar na hannun ’yan sanda kuma Kwamishinan ’yan sandan Jihar Imo, Taiwo Lakanu ya bayar da umarnin a mayar da mai laifin babban ofishin ’yan sandan jihar a kuma ci gaba da tsare shi har sai an gama yi masa bincike.
Wakilinmu ya ruwaito Onyekachi na fada wa manema labarai a harabar ofishin ’yan sandan cewa: “Bakar magana ta gaya mani kan kudi Naira 100, ni kuma na ji zafin haka, na mare ta. Nan take ba ta bari ta kwana ba, ta mayar min da martini. Nan take na ga ta zube kasa warwas.”
Ya ci gaba da cewa: “Ni fa ina son matata, ban yi haka don na kashe ta ba, ban kuma kashe ta da gangan ba, tsautsayi ne kawai da kuma karar kwana.”