✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe surukinsa saboda gona

Wani magidanci mai suna Maduabuchi Ede ya kashe surukinsa mai suna Kenneth Elom, a wani kauye cikin Jihar Ebonyita, bayan ya rafka masa katako a…

Wani magidanci mai suna Maduabuchi Ede ya kashe surukinsa mai suna Kenneth Elom, a wani kauye cikin Jihar Ebonyita, bayan ya rafka masa katako a kansa.
Da yake yi wa manema labarai karin haske dangane da lamarin, Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, George Okafor ya shaida wa Aminiya yadda labarin ta’addancin ya faru. Ya ce: “Matar mai laifin da suka rabu ce mai suna Schlastica take noma gonar mijin bayan sun rabu, ta tattara komatsenta ta dawo kauye amma duk da hakan ta kasance tsakaninsu ta ci gaba da yin noman doya a gonarsa.” Inji shi.
Duk wani matakin na a samu maslaha tsakanin matar da tsohon mijinta da abokinsa Augustine Nwakegwu ya yi ta hanyar tuntubar iyayen matar, domin su ja mata kunne, hakan ya ci tura duk da kokari da mahaifin matar ya yi, ya ce su dawo bayan kwana biyu domin a sasanta su amma suna kan hanyarsu ta komawa gida ne sai shi Kenneth ya ce wa abokin tafiyar su ratse su ji ta bakin uwar matar kafin su koma gida. Kafin su isa kauyen da surukar take dare ya yi masu a hanya amma tun da an san su sai aka buga kofarta, ta tashi daga barci ta bude kofa. Shi kuma kanen matar da ya ji suna gaisawa da uwarsu sai ya ce mata kada ta saurare su, ta rabu da su. Ya yi masu korar kare, ya ce su fita su bar masu gida.
kokarin su shiga motarsu su fice daga gidan ne shi kuma kanen matar ya dauko katako ya fafure su. Kenneth na kaucewa sai ya samu sa’ar kwace katakon, ya buga wa kanen matar ya fadi kasa warwas, somamme aka kai shi asibiti, daga can ne rai ya yi halinsa.
Jami’in ’yan sandan ya ce wanda ake zargi ya shiga hannu kuma bincike na nan yana ta kankama.