Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta cafke wani mutum da ake zargi da kashe abokinsa ta hanyar soka masa kahon dabba saboda ya ki ya saya masa giya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, SP Mohammed Ahmed Wakil, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Bauchi.
- APC za ta kaddamar da manhajar neman tallafin kudi daga ’yan Najeriya
- Gwamnati ta haramta wa baburan Adaidaita Sahu bin manyan titunan Kano
Ya ce rundunar ta kama mutumin mai suna Monday Ajasco, mai kimanin shekaru 29 da haihuwa, mazaunin garin Kafin Tafawa Bauchi a ranar 17 ga Nuwamban 2022,
Wakil ya ce kama mutumin ya biyo bayan bayanan da rundunar ta samu game da hannunsa a zargin aikata kisan kan.
“Binciken da ’yan sanda suka gudanar ya nuna cewa a ranar 16 ga watan Nuwamban 2022 da misalin karfe 11:00 na safe, wanda ake zargin ya je gidan giya a kauyen Bagel da ke Karamar Hukumar Dass, inda ya hadu da Abdulrazak Ibrahim mai shekaru 30 (wanda yanzu aka kashe), da wasu mutane kuma suna shan giyar a wani wurin shan giya a qauyen Bagel.
“Shi (wanda ake zargin) ya nemi Abdulrazak (marigayi) ya saya masa giya ya sha. Shi kuma marigayin ya ki.
“Hakan ya sa ’yar hatsaniya ta tashi a tsakaninsu da wanda ake zargin. Bayan wani lokaci suka yanke shawarar barin gidan giyar suka tafi gidajensu.
“Bayan wanda aka kashe ya tafi sai abokin mamacin ya ji kururuwa daga wajen abokin nasa daga nesa. Da isa wajen, sai ya gamu da abokinsa kwance cikin jini, yayin da wanda ake zargin yake tsaye kusa da wanda abin ya faru yana rike da kahon dabba a hannunsa.
“Ya kuma yi barazanar daba wa abokin wanda aka kashe wuka a lokacin da ya tambayi wanda ake zargin dalilin da ya sa ya yi haka.”
Kakakin ’yan sandan ya ce bincikensu kan lamarin ya nuna ce wanda ake zargin ya bi sawun wanda aka kashen ya kai masa hari ,ya soke shi a wuyansa da wani abu mai kaifi da ake zargin kahon dabba ne.
Ya ce a sakamakon, haka ya samu mummunan rauni inda aka garzaya da shi babban asibitin Dass, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Kakakin ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin a yi masa hukunci da zarar an kammala bincike.