✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe abokinsa a kan takalmi

Ya amsa cewa ya yi wa abokin nasa haka ne a matsayin ramuwar gayya

Wani matashi mazaunin Unguwar Saunar Nepa da ke Kano ya kashe abokinsa saboda abokin nasa ya sanya takalminsa.

Wanda ake zargin ya shaida wa manema labarai cewa ya aikata laifin ne a wani mataki na ramuwar gayya saboda marigayin mai suna Abubakar Abdulkarim ne ya fara kai masa sara.

“Muna zaune bayan mun yi alwala sai ya sanya takalmina, ni kuma sai na nemi ya cire sai ya ki don haka sai na zo na ture shi tare da kwace takalmina.

“Nan da nan sai ya dauko wani karfe ya kawo min suka da shi amma bai same ni ba.

“Ni ma kuma akwai wani karfe a jakata sai na fito da shi na soka masa a gefen cikinsa.

“Ban yi zaton ma ya mutu ba domin a kan idona wani abokinmu ya dauke shi zuwa kemis.

“Sai da dare ne mahaifina yake gaya min cewa ya rasu. Da safe kuma mahaifina ya dauke ni ya damka ni a hannun ’yan sanda.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa bayan da lamarin ya faru an dauki marigayin zuwa Babban Asibitin Muhammad Sanusi, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Kiyawa ya kara da cewa kasancewar wanda ake zargin ya amsa laifinsa, abin da ya rage shi ne su gurfanar da shi gaban kotu.