Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Kudancin Borno, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya sake sauke wasu ministocin da ba sa gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ya ce hakan zai taimaka wajen bai wa Tinubu damar cika wa ’yan Najeriya burikansu.
- Gobara ta yi ajalin ’yar shekara 80 a Ogun
- Zaɓe: Magoya bayan Ganduje sun shirya kawo tarnaƙi — Kwankwaso
Ndume, ya yaba wa Tinubu game da sauye-sauyen da ya yi a ministocinsa da kuma ƙirƙirar Ma’aikatar Ci-gaban Yankuna.
Ya bayyana waɗannan matakan a matsayin abin da ya dace, amma ya ce wasu ministocin har yanzu ba sa gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
A ranar Laraba ne, Tinubu ya kori wasu ministocinsa shida, sannan ya naɗa wasu sabbi bakwai, tare da sauya muƙaman wasu ministoci 10.
Ndume, ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu da ya shirya babban taron tattalin arziƙin ƙasa domin samar da hanyoyin da za su magance matsalolin tattalin arziƙin Najeriya.
Ya ce akwai tsofaffin mutane da ya kamata su jagoranci taron, irin su tsohuwar Ministar Kuɗi, Ngozi Okonjo-Iweala.
Sauran sun haɗa da tsohuwar Ministar Ilimi, Oby Ezekwesili, Mansur Muktar, Akinwumi Adesina, Aruma Oteh, da Tope Fasua.
A cewar Ndume, taron ya kamata ya mayar da hankali wajen samar da shawarwari da suka dace da yanayin Najeriya, maimakon dogara da tsauraran dokokin IMF da Bankin Duniya.
Ya ce, “Idan shawarwarin suna da kyau, ina ganin Shugaba Tinubu zai aiwatar da su, wanda zai taimaka wa ƙasar nan matuƙa.”
Ndume, ya kuma yaba wa Tinubu kan ƙoƙarinsa na rage kashe kuɗin gwamnati sakamakon matsalolin tattalin arziƙi, sannan ya shawarci sauran ɓangarorin gwamnati da su aiwatar da irin wannan doka.