Tsohon shugaban Majalisar Dattawa a Jamhuriya ta Biyu, Ameh Ebute, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rage farashin kayan abinci da na man fetur domin ’yan Najeriya su samu saukin rayuwa.
Ebute ya yi wannan kira ne yana mai nuna damuwa game da mawuyacin halin da tsadar man fetur ya jefa ’yan Najeriya a ciki.
Ya bayyana cewa babu yadda za a yi Shugaba Bola Tinubu da da tsare-tsaren gwamnatinsa su yi nasara, matukar al’ummar kasar suna fama da hauhawar farashin kayayyaki.
Don haka ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi tunani sosai ya sauke farashin man fetur a ƙasar nan.
- Kano: ’Yan majalisar APC sun yi mubaya’a ga Aminu Ado Bayero
- ASUU ta yi barazanar tsunduma yajin aiki kan ƙarancin albashi
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawarsa da manema labarai a taron ’yan majalisa da aka gudanar a Calabar, Jihar Kuros Roba.
“Ya kamata Tinubu ya yi aiki tuƙuru wajen shawo kan matsalolin da jama’a ke fama da su da kuma ya tabbatar da zaman lafiya, domin idan babu abinci, hakan yana iya haifar da fushi cikin sauƙi.
“Ina ba shi shawarar ya duba yiwuwar saukar da farashin kayan abinci da na man fetur.
“Da zarar farashin abinci ya ragu, farashin kayan abincin zai ragu.”
A cewarsa, Tinubu da manufar sabon tsarinsa na fatan samun ingantaccen sauyi da rayuwa mai daɗi, ba za su yi nasara ba a yanayin hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan.