A duk lokacin da na ji an ambaci kalmar rangadi, abin da ke fara zuwa a zuciyata bai wuce irin yadda ina dan makarantar Firamaren Nuhu da ke Kankiya ba ta cikin Jihar Katsina ta yau (1959 zuwa 1965), mu kanyi layi akan titin gari zuwa Kantin Kankiya muna daga tutar kasar nan ga babban bakon da ka shigo garin a zaman rangadi, bakon da a wancan bai wuce kodai marigayi Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Firimiyan tsohuwar Arewa na farko kuma na karshe, ko kuma Maimartaba Sarkin Katsina, Alhaji Sa Usman Nagwagwgo,(Allah Ya gafarta musu) a zaman sun shigo rangadi, wanda akasarin wadannan shugabanni sukan yi sau daya a shekara ko kuma a duk lokacin da wani muhimmin abu na kasa ya bijiro da ya kamata jama`ar ko talakawan sa ni, sannan kuma su san yadda za su tunkare shi da yadda za su ba da tasu gudummuwar, ta yadda al`amari ya kai ga nasarar da mahukunta suke bukata.
Sarakunan kasar Hausa a wancan lokaci, su aka fi sa ni da fita rangadi, akalla sau daya a shekara, musamman a irin wannan lokaci da ake kokarin shiga kakar amfanin gona, lokacin da suke bayyana wa kowane hakimim gunduma da dagatansa da masu ungunninsa da sauran jama`ar gundumar irin yawan kudin haraji da jangalin da ake tsammanin wannan gundumar ta tara, ta kuma biya cikin baitalmalin En`en din masarautar sarkin, kan hada da sanar da talakawansa a cikin rangadin ranar da za a kafa sikelin awon amfanin gona da irin farashin da za a sayi amfanin gonar wannan shekarar, irin su gyada da auduga da makamantansu.
Ba wai batun sanya haraji ko jangali kan sa sarakuna rangadin masarautunsu ba, kamar yadda na fadi a baya, bijirowar wasu muhimman batutuwa da Mahukunta ke son sanar da jama`ar su kamar batun daukar yara makarantun Firamare, ko a kan yin rigakafin wasu cututtuka da aka samu labarin bullarsu da yadda za a yi maganinsu bayan sun bulla, da makamantan muhimman bukatu kan sa sarakuna fita rangadi a wancan lokacin. A yau ba haka batun ya ke ba, inda duk ka ga sarki ko hakimi a cikin masarautarsa a birni da karkararta, za ka taras raka gwamnan jiharsa ya yi, in kuma tafiyar kansa ce, za ka tarar bude makarantar Islamiyya ko masallaci aka gayyace shi, ko kuma ya fita ne bisa ga umurnin gwamnan jiharsa, har ta kai fagen yanzu sai a nada sabon Sarki, har ya gama zamaninsa, bai fita rangadin masarautarsa ba .
Abin da ya sa na bijiro da shawarar ”Ya kamata Sarakuna su farfado da tsarin rangadi” a wannan makala ta yau bai wuce irin jawaban da suke fitowa daga bakin Maimartaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, Sarki na 14, a Daular mulkin Fulani a Kano, wanda ya hau kan karagar mulkin masarautar Kano a ranar 08-06-14, bayan mutuwar Sarki Alhaji Ado Bayero. Kuma a karon farko a ranar 08-06-14, Sarki Muhammadu Sanusi II, ya fara rangadin Masarautarsa, da gundumar danbatta ko in ce karamar Hukumar danbatta (kowace masarautar Hakimi a Jihar Kano tana zaman Majalisar karananan Hukumomi ce). Zuwa yanzu bayan karamar Hukumar danbatta,Sarkin, ya ziyarci gundumomi ko kananan Hulumomin Makoda da Ungogo da Dawakin Kudu da Warawa da Kumbotso, rahotannin da suke bayyana a cikin rangadin, sun tabbatar da cewa har kwana biyu ya yi a garin danbatta.
A duk inda Sarki Malam Sanusi II, ya ziyarta zuwa yanzu maganganu iri daya ya ke ta jaddadawa ga talakawansa, maganganun da suka jibanci irin halin zamantakewar da talakawan suke ciki, kamar batutuwa na tabarbarewar matakan tsaro da neman ilmi kowane iri (na addini da na zamani) da ilmin `ya`ya mata da batun kiwon lafiya da na matsayin tattalin arzikin kasa da dai sauran matsalolin rayuwa da na zamantakewa da ake ciki a kasa baki daya.
Alal misali jawabin Sarki Muhammadu Sanusi II, yakan fara da tunatar da shi kansa da sauran jama`a, muhimmancin jin tsoron Allah a dukkan abin da za su yi a rayuwa da yin da`a ga Allah da ManzonSa SAW. Yakan tunatar da talakawan yanayin tabarbarewar tsaro da kasa ta ke ciki, da neman kada su rinka amincewa da duk wata bakuwar fuska da suka gani a tsakankaninsu, to, su rinka gaggauta kai rahoto ga mahukuntansu. Akan fannin neman ilmi Mai martaba San Kanon, yakan jaddada muhimmancin da zai sanya jama`a su tashi tsaye haikan wajen ganin sun nemi ilmi na addini da na sa`a akan su kansu da `ya`yansu, yana mai jaddada wajibcin yin hakan ga al`ummar musulmi, saboda kasancewar ilmi shi ne tushen ci gaban kasa da jama`arta, rashin shi kuma shi ke kawo akasin hakan da kuma wulakanci da kaskanci, inda ya nemi iyaye da lallai su rinka tura `ya`yansu mata zuwa makarantu maimakon dora masu tallace-tallace, ko tura su aikatau a manyan birane.
A yayin rangadin, Mai martaba San Kanon ya kan karrama `yan asalin kananan hukumomin da ya ziyarta, walau `yan bokonsu ko masu hannu da shunin cikinsu da lambobin yabo akan irin yadda irin wadannan mutane suke jibantar tallafa wa mutanensu masu rauni, ta fannoni daban-daban na rayuwa, inda yakan kara da neman irin wadannan mutane da su ci gaba yin irin wadannan ayyukan alheri, musamman na daukar nauyin karatun marayu tun daga makarantun Firamare har ya zuwa makarantun gaba da Sakandare da wadanda suke jibantar matsalolin matan da mazajensu suka mutu. Ya kan kuma koka akan irin yadda mace-macen aure suka fi yawaita a Jihar Kano, da annobar da hakan ke haddasawa wajen ruguza iyali, al`amarin da ya ce rashin hakuri ke kawo haka. A nan sai ya yi fatan jin labarin garin da za a shekara sukutum a cikin masarautarsa ba tare da an samu mutuwar aure ba.
Yakan kuma yi tsokaci akan kula da matakan kiwon lafiyar jiki da ta muhalli da yin allurar rigakafin cututtukan da sukan addabi kananan yara, tare da taya Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da mutanen jihar da ma kasa baki daya akan yadda aka shafe shekara daya cur ba tare an samu ko da yaro daya da ya kamu da cutar shan inna a kasar nan ba. Wani batu mai muhimmanci da ya kamata Sarkin ya rinka janyo hankalin masu hannu da shuni, shi ne, muhimmancin fitar da zakka, musamman ta kudi da bayar da ita ga wadanda Allah Ya ce a baiwa. Duk da muhimmancin fitar da zakka kasancewarta daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar, da yadda Allah Ya azurta Jihar Kano da mutane masu wadata fiye da kowane birni a nan Arewa, rahotanni sun tabbatar da cewa zakkar da hukumomi suke tattarawa da rabawa a jihohi irin su Sakkwato da Jigawa sun fi ta Jihar Kano.
Don haka cikin wannan rangadi da ma kodayaushe nike ganin akwai bukatar Maimartaba San Kanon, ya rinka tunatar da jama`arsa akan muhimmancin su rinka fitar da zakka da ba da ta ga Hukumar Zakkah da Hubusi ta jiha. Haka su ma sauran Sarakunan Musulunci da sauran Sarakuna duk inda suke nike ganin ya kamata su farfado da rangadin masarautunsu, musamman kasancewar yanzu rangadin ba na fasa haraji da Jangali ba ne, sai don fadakarwa da musabaha da talakawa, talakawan da har gobe suke da biyayya da shaukin ji da saduwa ta ra`ai-ra`ai da sarakunansu.
Ya kamata sarakuna su farfado da tsarin rangadi
A duk lokacin da na ji an ambaci kalmar rangadi, abin da ke fara zuwa a zuciyata bai wuce irin yadda ina dan makarantar Firamaren…