Shugaban Sashen Hausa na gidan Rediyon FM Alternatibe dake birnin Yamai a Jamhurirryar Nijar, Souley Mage Rejeto, ya bukaci Jami’ar Bayero Kano da ta karrama Ado Ahmad Gidan Dabino da digirin girmamawa.
Ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da wata mukala mai shafi takwas a wajen taron da aka shirya don taya Ado Ahmad murnar samun lambar yabo ta kasa MON da kuma cikarsa shekara 50 da haihuwa.
Souley ya ce Gidan Dabino, marubuci ne kuma dan jarida wanda ya yi gwagwarmaya a fagen rubutun Hausa da aikin jarida, wanda hakan ta sa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karrama shi, inda ya ce ya kamata jami’oin kasar nan, musamman ma Jami’ar Bayero ta Kano ta karrama shi ta hanyar ba shi digirin girmama saboda yadda ya yi wa adabin Hausa hidima a Najeriya da wasu kasashe na Afirka.
Ya ce Ado ya ba da gudunmawa sosai a bangaren rubutun Hausa da kuma tsayawa kan kafarsa wajen ganin wannan yare na Hausa ya samu daukaka a fadin duniya, domin ko daliban ilimin harshen Hausa a wasu kasashen Turawa na zuwa wajensa don nazarin wasu littafai.
Kamar yadda ya ce, Ado ya fara rubuce-rubuce da aikin jarida ne sama da shekaru 32 da suka gabata, inda ba a iya Najeriya kawai ya tsaya ba, yakan je gidan Radiyo mai zaman kansa na Freedom da ke Kano da Shukura FM da ke Damagaran a Nijar don ba da gudumawarsa lokaci zuwa lokaci.
Taron dai ya gudana ne a gidan Malam Aminu Kano da ke Mambayya a Gwammaja, inda shehunnan malaman boko irin su Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa Abdalla Uba Adamu da Farfesa Yusuf Adamu da Farfesa Salisu Yakasai da sauransu suka bayyana irin gudunmawar da Gidan Dabino ya bayar a fagen rubutu da aikin jarida.