✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata gwamnati ta tallafa wa bangaren kiwon kaji – Mista Etah

A yayin da farashin kaji da na kwai ke kara yin sama sakamakon karuwar bukatarsu musamman a loktuan bukukuwan karshen shekara. Wani da ya jima…

A yayin da farashin kaji da na kwai ke kara yin sama sakamakon karuwar bukatarsu musamman a loktuan bukukuwan karshen shekara. Wani da ya jima a harkar ya yi wa Aminiya bayanin a kan sirrin da ke cikin harkar kiwon kaji da yadda za a ci gajiyarta

 

 Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Henry Etah. Ni dan asalin Jihar Kuros Riba ne, sai dai ina zaune a garin Keffi da ke Jihar Nasarawa ne kuma ina aiki da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke garin. Ina da  digiri a  harkar kasuwanci daga Jami’ar Jihar Legas, sai digiri na biyuc  daga Jami’ar Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Owerri.

Yaya aka yi ka samu kanka a sana’ar kiwon kaji?

Na fara sana’ar ce bayan na gama makarantar sakandare a 1985 a can gida. Sai na bar kauyenmu zuwa yankin Ibo wadanda makwabtanmu ne. A can na samu aikin kula da kaji na wani mutum mai suna Rufus Obaja da ke da makeken wajen kiwon kaji. To daga nan ne na fara sha’awar sana’ar, kasancewar yana karfafa min gwiwa. Sana’a ce mai bukatar karfin hali kuma kafin in fara aiki a wajensa wadansu sun riga ni amma bayan dan lokaci sai su ajiye aikin. Hakan ya taimaka min kwarai a rayuwa kuma da kudin da nake samu a wajen ne, na yi rajistar shiga jami’a har na bude wajen kiwo na kaina.

Kamar da kaji nawa ka fara naka kiwon? 

Kasan akwai nau’o’in kaji uku: Masu saurin girma (Broilers) da masu yin kwai (Layers) sai marasa daraja wadanda ba su da saurin girma kuma ba sa kwai (Cockerel). To masu yin kwai da masu saurin girma suna da tsada. Sannan sai an yi musu hidimar wata shida kafin su fara zubi. Su kuma masu saurin girma duk da cewa mako bakwai ne kawai suke yi a sayar da su, suna bukatar abincin kamfani ga kuma yawan ci, to ba ni da kudin da zan iya kulawa da wadannan nau’o’i biyun. Sai na gwammace kiwon kokirel wadanda ba su da tsada wajen saye ga kuma saukin kiwo kasancewar bayan kamar wata daya da fara kiwo a iya sake su su rika hadawa da abinci da kansu a wurare kamar karkara. To sai na je birni na saro dubu daya, na yi rainonsu na tsawon mako biyu na fara sararwa ga jama’ar kauye, kuma kan a ce sun kai wata daya a gida sai na samu nasarar sayar da su baki daya. Haka na rika yi yana ba ni riba. A cikin haka na dauki dawainiyar karatun digirna na farko, na yi aure har na sake digiri na biyu.

Wane karin bayani za ka yi a kan nau’o’in kajin nan uku da ka ambata?

Masu daraja na farko su ne masu yin kwai. Sun fi kawo kudi sai dai suna bukatar jari sosai saboda za a yi ta yi musu hidima har tsawon wata 6 kafin a fara cin gajiyarsu. Sai masu saurin girma da ke da aukin nama. Su wadannan an fi cin gajiyarsu sosai a lokutan bukukuwa kamar na Kirsimeti da Ista, sai kuma lokacin Sallah. Ana kiwonsu na tsawon mako bakwai lokacin sun kosa sai a sayar da su. Kuma yana da kyau ka auna lokacin da zai dace da kosawarsu sai ka fara kiwonsu wato a lokacin da ya rage kamar makonni bakwai ke nan ko takwas kafin lokacin bikin da ake son a sayar da su. Sai kuma na karshe su ne wadanda ba sa yin kwai kuma ba su da saurin girma, za su kai kamar wata 4 kafin su kosa. Wadannan sun fi karbuwa a yankunan karkara saboda saukin raino ga shi kuma suna ganinsu da kwari kusan kajin gida.

Bayan kyankyasa wace dabara ce ake amfani da ita wajen rarrabe su?

Baya ga amfani da ilimin kyankyasa da suke da shi, wani abu da ya bayyana a fili gamu masu hulda da su shi ne, a bangaren kaji masu launin baki, gashin matansu gaba daya baki ne, a yayin da na mazansu kuwa yana da ’yar alamar ta ratsin fari a kai daga bangaren goshi, kuma ita ce za ta ci gaba da bayyana ta ko’ina idan suka girma ka ga launi baki da fari dabbare-dabbare ta ko’ina. Akwai kuma nau’in kaza mai namiji fari mace kuma ruwan kasa. Mazan suna fara girma za ka ga alamar ratsin ruwan kasa a jikin fuka-fukansu biyu. Duk wadannan nau’o’in kajin biyu ba masu saurin girma ba ne. Sai kuma nau’i na karshe wanda a cikinsa ne kadai ake samun masu saurin girma. Shi gaba dayan jikinsa fari ne kuma daga kyanykasarsa ya dara sauran nau’ukan kajin nauyi da kaurin kafa.

Yaya maganar ciyarwa ko akwai wani bambanci a abincin da suke ci?          

Ga kaji masu yin kwai wadanda su ne masu daraja ta 1, abincin farko da ake fara ba su daya yake da na kaji marasa girma wanda ake kiransa da suna abincin ’yan tsaki. Za a yi ta ba su shi har zuwa tsawon mako 6, kuma daga nan sai a fara ba su na girma har zuwa lokacin da suka kai wata 6. Su na fara yin kwai sai a sauya musu nau’in abinci daga wanda ke girma zuwa wanda zai fi dacewa da hali na jego. Kuma shi ne za a yi ta ba su har karshen rayuwarsu. Bayan sun kai kamar wata 9 suna zuba kwai daya a kullum, za su fara ja baya su rika fashi har ya kai suna yin kwai sau daya a kwana uku.

Su kuma masu saurin girma kuma masu daraja ta biyu suna bukatar abinci babu hutawa a tsawon sa’o’i 24. Abincinsu ya kasu kashi 2 ne, akwai na farawa da za su ci tsawon mako 3, sai na karkarewa mako 4 lokacin da za a sayar da su.

Su kuma na karshe wato zakaru kuma marasa girma, ana fara musu da abinci iri daya ne da na masu kwai na tsawon mako 6 zuwa 7 daga nan kuma sai a koma ba su na girma har zuwa lokacin da za a yanka su kamar yadda na yi bayani a baya suna kai wata 4, kafin su kai munzalin ci.

Wane lokaci ne mafi dacewa da sayar da su?

Ga masu saurin girma mako 7 ne kuma dole ka yi tanadin kasuwar kada-ta-kwana don ganin ka sayar da su a lokacin saboda duk wani jinkiri da za ka yi zai fi kai ka ga asara maimakon riba, saboda sun kai munzalin girma kuma nauyin da za su kara bai taka kara ya karya ba idan aka yi la’akari da abincin da za su ci. Su ko marasa girma da sun kai wata 4 sai ka fara sayar da su sannan wadanda ba su samu shiga ba nan take za ka rage tsadar abincin da kake ba su ta hanyar surkawa da abincin gida maimakon na kamfani zalla.

Sannan a bangaren kaji masu kwai wannan ba ka da matsala saboda a kullum a cikin kawo kudi suke. A gaskiya ma bukatar kwai da ake da ita a yanzu ta zarce adadin wanda ake samarwa, wannan  ya sanya su a matsayin nau’i mafi daraja saboda yawan masu bukatar kwai, kamar masu shayi da masu gidajen abincin zamani da makarantu da daidaikun mutane. Idan suka fara kwai za a ci gajiyarsu har tsawon wata 9, daga nan sai girma ya fara shafar yawan kwan da suke yi, alhali cin abincinsu na nan yadda yake bai ragu ba. Sai dai idan suka kai wannan mataki na manyanta kwansu ya fi girma, shi ne ake kira “Jumbo size” haka za su kasance har su cika shekara 1 da wata 6 suna kwai. To a wannan lokaci sai a sayar da su.

Ko akwai magunguna da ake ba kaji daga yarintarsu zuwa girma?

Akwai littafi na musamman a matsayin jagoran mai kiwo a dukan al’amuransu ciki har da bangaren magani. Haka kuma mutum zai iya samun likitan dabbobi a bangaren kaji don ya rika kawo masa ziyarar sa ido da za ka iya shiryawa da shi a kan duk mako ko wata ko a lokacin da bukatar gaggawa ta bijiro.  Zai ba ka shawarwari a kan magungunan da ake ba su kamar na lokacin da suke kasa da mako 1 da lokacin da za ka ba su na rigakafin kwayoyin cuta, ko idan aka fuskanci matsalar barkewar wata cuta.

Yaya za ka bayyana kimar sana’ar kiwon kaji a kasar nan?

A gaskiya Allah Ya albarkaci kasarmu da dukan damar da ake bukata don yin kiwo. Na farko yanayinmu matsakaici ne bai da bala’in zafi kuma bai da dusar kankara, wanda dukansu ke bukatar wani tanadi na musamman. Ga kuma arzikin yawan jama’a wanda ba sai mun kai hajarmu zuwa wata kasa ba, gida kadai ta ishe ka kasuwa. A dalilin haka zan iya bayyana sana’ar a matsayin wadda za ta fi kowacce ba da riba bayan ta mai da kasar nan ta dogara da ita.

Wane alheri ka samu a wannan sana’a?

A gaskiya sana’ar kiwon kaji ta yi min komai. Kamar yadda na bayyana a farko a cikinta na yi digiri na farko da na biyu na kuma yi aure. Kai hatta ma wannan aiki da nake yi a yanzu ta dalilinta ce na samu. Har yanzu ina yin ta saboda matata da ’ya’yana da dangi da muke tare suna gudanar da ita kan yadda na tsara musu. Ina kuma da niyyar fadada ta a duk lokacin da na yi ritaya.

 A dukan sana’a ba a rasa matsala shin wacce ce ta kiwon kaji?

Idan a a yi rashin dace mai yi ya shige ta ba tare da cikakken ilimi a harkar ba, to za a fuskanci asara. Ilimin nan ya hada da na sanin irin nau’in da ya kamata ya yi kiwo a waje da kuma a lokaci. Misali idan mutum yana yankin karkara kajin kokirel wadanda ba sa saurin girma ko kuma kwai su ne suka fi dacewa da wajen kasancewar akwai fili a cikin sauki. Sannan a birni kuma za a iya kiwon na kwai kasancewar akwai masu saya. Ga masu saurin girma kuwa dole ne a yi la’akari da lokacin da za a sayar da su da daraja. Sannan a samar musu waje mai yanayin dumi a lokacin da suke kanana ta hanyar rufe ragar da kuma tanadin dumi na fitila ko na gaushi, saboda idan iska mai sanyi tana busa su suna iya kamuwa da cutar nimoniya su mutu. Wannan ya danganci yanayin da ake ciki da kuma nau’in kajin.  Ga masu saurin girma a yanayi irin na damina da ake ciki yanzu, za su kasance a waje mai yanayin dumi har tsawon mako 3, ko  kwana 10 idan a lokacin da ba na sanyi ba ne. Idan kuwa marasa girma ne ko masu kwai, za a ajiyesu a waje mai dumi kamar mako 4 idan a lokacin sanyi ne, ko mako 3 a lokacin da ba sanyi. Dumin zai samar musu kishi da yunwa, su bukaci abinci da shan ruwa a kai-a-kai tare da kada fuka-fukansu wanda hakan zai ba su saurin girma, maimakon su kasance a cikin takura idan sanyi na damunsu. To bayan tsawon wannan lokaci, sai a sauya musu waje zuwa inda yake da budaddiyar raga gaba da baya suna samun iska gwarrgwadon bukata saboda sun fara girma. Idan aka samu akasi a nan ma, sai ka ga an rasa su.

A karshe wane kira za ka yi ga gwamnati kan kiwon kaji?

Ya kamata gwamnati ta sani burinta na inganta sha’anin noma ba zai kammala ba har sai ta hada da bangaren kiwo wanda na kaji na ciki. Babban matsalar da muke fuskanta a harkar kiwon kaji ita ce ta tsadar abincinsu. To ya zama wajibi gwamnati ta samar da kanana da matsakaitan injunan sarrafa abincin kaji tare da rabawa ga kungiyoyin masu kiwonsu a kauyuka da birane don karya farashin abincinsu. Buhunsa guda da shekaru kadan baya kafin shiga matsalar tsadar abinci da muke saya a kan Naira  2400, a yanzu ya koma Naira 3800. Babban abincinsu masara ce, za a iya sayenta a lokacin da amfanin gona ya wadata a sarrafa ta sai kuma wasu sinadarai da ake karawa wadanda bukatarsu kadan ce a surka. Haka farashin ’ya’yan kaji na tsada. Misali masu saurin girma da ba su wuce Naira dari ba, idan lokaci na kiwon Kirsimeti ya zo sai a kara farashinsu zuwa Naira 350. Na kwai kuma dama a kullum suna da tsada ana sayar da su ne a kan Naira 250. MaSU saukinsu su ne kaji marasa saurin girma a kowane lokaci ana sayar da su ne a kan Naira 20 zuwa 30. Dama su ribar kafa ce, saboda idan aka kyankashe kwai 500 za a samu rabi masu kwai ne wadanda su kadai za su fitar da kudi su ba da riba. Sannan rabin 500 din kuma kaji ne marasa girma, su wadannan ana sayar da su a kan farashi kasa da na kwai wato Naira 20 kacal. A shekarun baya zubar da su ma ake yi kamfani bai bukatarsu, to a yanzu ne idan ana da aladu sai a dafa su a ba su idan sun yi kwantai.